Majalisa tayi barazanar kama Shugaban Hukumar EFCC

Majalisa tayi barazanar kama Shugaban Hukumar EFCC

- 'Yan Majalisa na shirin bada umarni a kama Shugaban EFCC

- Majalisa ta kira Magu ya bayyana a gaban ta amma bai yi ba

- Matar tsohon Shugaba Jonathan ce ke karar Shugaban na EFCC

Mun samu labari cewa 'Yan Majalisar Wakilan Tarayya na shirin bada umarni a kama Shugaban Hukumar EFCC Ibrahim Magu.

Majalisa tayi barazanar kama Shugaban Hukumar EFCC

Shugaban Hukumar EFCC Ibrahim Magu

Matar tsohon Shugaban kasa Jonathan watau Patience Jonathan ce ke karar Shugaban na EFCC bayan Hukumar ta rufe asusun bankin ta inda tace abin ya wuce gona da iri. A dalilin haka ne Uwargidar Jonathan din ta kai karar Hukumar da ke yaki da yi wa tattalin kasar zagon-kasa.

KU KARANTA: INEC tace za ta yi wa Dino kiranye bayan hukuncin Kotu

Honarabul Uzoma Abonta wanda shi ne Shugaban kwamitin jin kukan jama'a a Majalisar ya bayyana cewa Shugaban EFCC Magu ya saba masu bayan sun nemi ya bayyana a gaban ta bai kuma yi ba. Yanzu haka Majalisar za ta sa a tursasa Magu ya bayyana a gaban na ta ko a kama sa.

Majalisa dai tayi kira ga bankunan da su ka garkame asusun tsohuwar Uwargidar kasar Patience Jonathan da su yi maza su bude su.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000
NAIJ.com
Mailfire view pixel