Gwamnatin Sakkwato ta amince da sabon doka don karfafa yunkurin aikata laifuka

Gwamnatin Sakkwato ta amince da sabon doka don karfafa yunkurin aikata laifuka

- Majalisar zartarwa na Sakkwato ta amince da dokar da za ta taimaka wajen inganta yunkurin magance laifuka

- Dokar ta bukaci al'ummomi samar da kayan aiki da leken asiri don tallafa wa hukumomin tsaro

- Majalisar ta kuma amince da tsarin bayar da agaji a harkokin kiwon lafiya a jihar

Majalisar zartarwa a jihar Sakkwato ta amince da dokar da za ta taimaka wajen inganta yunkurin magance laifuka a fadin jihar.

Idan majalisar dokokin jihjar ta amince, dokar za ta tabbatar da cewa al'ummomin za su samar da kayan aiki da leken asiri don tallafa wa hukumomin tsaro gudanar da aikin su.

Wata sanarwa a ranar Litinin wanda babban mai shari'a a jihar kuma kwamishinan shari'a, Sulaiman Usman ya bayyana, ya bayyana hanyoyi da dama kamar kula da yanki, aikin kula da al'umma wanda za a iya amfani da ita don rage laifuka.

Gwamnatin Sakkwato ta amince da sabon doka don karfafa yunkurin aikata laifuka

Gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal

Majiyar NAIJ.com ta tabbatar da cewar, wadannan hanyoyi za su haɗa da mazauna da kuma al'ummomi don magance abubuwan da suke taimakawa wajen aikata laifuka da kuma rashin biyayya ga doka da tsara.

KU KARANTA: Majalissar dattawa za ta binciki shugaban NNPC, Baru akan zargin da Kachikwu yayi masa

Bisa ga wannan sanarwa, majalisar ta kuma amince da tsarin bayar da agajin harkokin Kiwon lafiya a jihar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa
NAIJ.com
Mailfire view pixel