Zaben 2019: Yakin neman zaben Atiku Abubakar ya kankama a kudancin Najeriya

Zaben 2019: Yakin neman zaben Atiku Abubakar ya kankama a kudancin Najeriya

Kawo yanzu dai labaran da muke samu na nuni ne da cewa gangamin yakin neman zaben tsohon mataimakin shugaban kasa kuma Wazirin Adawa Alhaji Atiku Abubakar na tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2019 tuni ya fara kankama a kudancin kasar nan.

Labaran da muka samu dai sun bayyana cewa daya daga cikin kungiyoyin da ke yi masa aiki mai suna United Atiku Abubakar Support Group a turance tuni ta kammala shire-shiren ta na kaddamar da shugabannin ta a yankin kudu-maso kudancin kasar.

Zaben 2019: Yakin neman zaben Atiku Abubakar ya kankama a kudancin Najeriya

Zaben 2019: Yakin neman zaben Atiku Abubakar ya kankama a kudancin Najeriya

KU KARANTA: Da alama sata cikin jinin yan Najeriya take

NAIJ.com ta samu dai cewa shugaban kungiyar na shiyyar Kwamared Godswill Mathew ya shawarci matasan yankin da su marawa dan takarar baya domin shi ne kawai ke son su da ci gaba.

Haka kuma shugaban na kungiyar a shiyyar ya kuma bayyana tabbacin sa ga yan shiyyar cewa Atiku Abubakar shine kawai zai iya lashe zaben mai zuwa don kuwa duk yafi sauran kwarewa da kuma jajircewa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel