Fasaha! Yadda wani matashi a Zamfara ke kera injinan sarrafa shinkafa

Fasaha! Yadda wani matashi a Zamfara ke kera injinan sarrafa shinkafa

Hakika arewacin Najeriya Allah ya albarkace mu da hazikai kuma matasa masu dumbin fasawa a kusan ko wane lungu da sako na yankin.

Nan ma dai mun samu ne daga majiyar mu yadda wani matashi mai suna Injiniya Ilyas Nazifi yake kerawa mutanen yankin yan kasuwa da ma sauran masu hannu-da-shuni injinan sarrafa shinkafa.

Fasaha! Yadda wani matashi a Zamfara ke kera injinan sarrafa shinkafa

Fasaha! Yadda wani matashi a Zamfara ke kera injinan sarrafa shinkafa

KU KARANTA: APC bata cancanci zama jam'iyya ba - Buba Galadima

NAIJ.com ta samu dai cewa Injiniya Ilyas Nazifi ya amfata cewa ya zuwa yanzu dai shi da sauran wadanda ke yin aiki a karkashin sa sun samu nasarar kera injunan sarrafa shinkafar a kimanin kamfunnan da suka tasar ma 50 a fadin kasar.

Haka ma kuma Injiniyan ya bayyana cewa ya zuwa yanzu babu inda aka taba kiran su aka ce masu injinan sun samu matsala bayan sun kamma hada masu su.

Hazikin matashin har ila yau ya kara da cewa kawo yanzu ma dai har sun shiga wata yarjejeniya ta musamman da jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria don ganin an kara habaka sana'ar ta sa domin al'umma da dama su anfana.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel