Gwamnati ba za ta dawo da Diezani Najeriya ba - Inji Malami

Gwamnati ba za ta dawo da Diezani Najeriya ba - Inji Malami

- Babban mai shari'a ta tarayya, AGF ya ce babu bukatar gwamnatin tarayya ta dawo da Misis Diezani Alison-Madueke

- Malami ya ce gwamnatin Birtaniya ta riga ta dauki matakan da ta dace kan batun

- AGF ya ce gwamnati ta na kokari wajen magance cin hanci da rashawa a Najeriya da waje

Babban mai shari'a ta tarayya, AGF, Abubakar Malami (SAN), ya ce babu bukatar gwamnatin tarayya ta dawo da tsohon ministan albarkatun man fetur, Misis Diezani Alison-Madueke zuwa Najeriya don fuskantar shari’a a kan cin hanci.

Majiyar NAIJ.com ta tabbatar da cewar, Malami, a wata ganawa da manema labarai a harshen Hausa a fadar shugaban kasa, Abuja, ya ce ba za a yi hakan ba tun da Ingila na bincikar tsohon ministan.

Alison-Madueke ta bukaci babban kotun tarayya a Legas cewa ta tilasta AGF ya dawo da ita Najeriya daga Birtaniya, inda ta yi tafiya zuwa jim kadan bayan barin ofishin a shekarar 2015.

Gwamnati ba za ta dawo da Diezani Najeriya ba - Inji Malami

Babban mai shari'a ta tarayya, AGF, Abubakar Malami (SAN)

Ta ce ta so ta bayyana a kotun Najeriya don kare laifin cin hanci da aka yi zargi ta aikata na naira miliyan 450, inda aka ambaci sunanta.

KU KARANTA: Kasafin kudin 2017: Gwamnatin Tarayya tace ba ta da kudi

Amma Malami ya ce gwamnatin Birtaniya ta riga ta dauki matakan da ta dace kan batun.

Ministan ya ce idan gwamnatin tarayya ta ga dalilin da zai sa a dawo da tsohon ministan, ba za ta jinkirta yin haka ba.

Malami ya ce gwamnati ta na kokari wajen magance cin hanci da rashawa a Najeriya da waje.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Daukan dala ba gammo: Wani jami’in Soja ya ɗirka ma Mahauci harsashi a kan cin hancin N500

Daukan dala ba gammo: Wani jami’in Soja ya ɗirka ma Mahauci harsashi a kan cin hancin N500

Illar cin hanci: Sojan Najeriya ya bindige wani Mahauci a kan ya hana shi N500 na goro (Hoto)
NAIJ.com
Mailfire view pixel