Gwamnatin tarayya zata binciki fitar da gurbatattun 
doya zuwa kasashen ketare

Gwamnatin tarayya zata binciki fitar da gurbatattun doya zuwa kasashen ketare

- Gwamnatin tarayya zata binciki fitar da gurbatattun doya zuwa kasashen ketare

- Najeriya ta fara fitar da doya don a daina dogaro da man fetur da farfado da tattalin arzikin kasa

- Kudin shinkafa zai sakko zuwa watan gobe

Gwamnatin tarayya zata binciki fitar da gurbatattun doya daga Najeriya zuwa kasashen Amurka da Ingila, Ministan harkokin noma, Mista Audu Ogbeh ya shaida.

A ranar 29 ga watan Yuni ne Najeriya ta fara fitar da doya zuwa kasashen turai domin a samu a daina dogaro a kan man fetur domin koma bayan tattalin arzikin kasar da aka shiga. Daga filin jirgin sama na Apapa da ke jihar Legas ne Mista Ogbeh ya tabbatar da fitar da doyar na farko a kasa.

Gwamnatin tarayya zata binciki doyoyi gurbatattu da ake fitarwa zuwa kasashen turai

Gwamnatin tarayya zata binciki doyoyi gurbatattu da ake fitarwa zuwa kasashen turai

Ministan ya shaidawa majilasar FEC bayan taron da tayi da Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta cewa wajibin ma’aikatar sa ne ta yi binicke a wannan lamarin. Ya yi magana a kan doyar da ake fitar wa kasar waje wanda suke gurbatattu. Ma’aikatar zata yi bincike a kampanonin da suke da hannu a safarar doyar.

Sannan ministan ya shaida musu cigaban da aka samu a harkan noma, don manoman shinkafa a wannan shekarar suna sa ran sayar da buhun shinkafa a farashi mai sauki.

DUBA WANNAN: Majalisar dattijai zata binciki korar sojoji 38

Ministan ya shaida yanda suka damu a yadda kudin shinkafa ya tsefe domin kuwa ita ce abinicin da aka fi ci a Najeriya.

'Zuwa watan gobe muna sa ran kudin shinkafa zai sakko bayan tattaunawa da muka yi da manoman shinkafa' ministan ya shaida.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel