Mu na kan yaki da masu Jihadi: Ministan Faransa

Mu na kan yaki da masu Jihadi: Ministan Faransa

- Kasar Faransa ta fitar da sabon doka da zai saukaka masu wurin kulle masallatai da ke yada kalamai na kiyayya

- Ministan Cikin Gida na kasar mai suna Gerrard Columb ya ce dole kasar ta kare kanta daga barazanar 'yan ta'adda da tsagera

- Majalisar kasar ta bai wa Ministan ikon kulle wuraren ibada da ake zargin su da ta'addanci

Majalisar Kasar Faransa ta fitar da wata doka a kan ta'addanci wanda zai karfafa da saukaka ma hukumar 'yan sanda wurin kulle masallatai masu yada kalaman kiyayya.

Kafin fitar da dokar, Gerrad Collomb wanda shine Ministan Cikin Gida na kasar ya ce har yanzun suna kan yaki da 'yan ta'addan haure da tsegeran cikin gida. Daga 2015 zuwa yanzun rayukan mutane fiye da 240 sun salwanta.

A kwanan nan wani dan Jihadi mai suna Ahmed Hanechi ya kwada kabbara a bakin tashar jirgin kasa kafin ya daba ma wasu mata biyu wuka wanda ya yi sanadiyar mutuwar su.

Mu na kan yaki da masu Jihadi: Ministan Faransa

Mu na kan yaki da masu Jihadi: Ministan Faransa

Ministan ya ce 'yan Majalisa sun lura akwai bukatuwan kare kasa daga barazanar da 'yan ta'adda ke yi wa harkan tsaro, wanda kuma dole a yi shi ba tare da danne hakkin kowa ba.

DUBA WANNAN: Najeriya zata shiga cikin halin Kakani-kayi idan har bata samar da tattalin arzikin da ba na man fetur ba - Ezekwesili

Don haka an bai wa Ministan karfin iko hana shige da fice kai tsaye a wurin da akwai wata barazana. Ministan kuma na da ikon kulle masallatai da sauran wurin ibada da ake zargin su da ta'addanci. Su kuma jami'an tsaro suna da ikon shiga wurare kai tsaye don gudanar da bincike.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000
NAIJ.com
Mailfire view pixel