Gwamnatin Yobe zata kashe Naira miliyan 770 wajen samar da ingatattun kayan aikin asibiti da makarantu

Gwamnatin Yobe zata kashe Naira miliyan 770 wajen samar da ingatattun kayan aikin asibiti da makarantu

- Gwamnatin Yobe zata kashe miliyoyin kudi don samar da ingatattun asibitoci da makarantu a jihar

- Gwamnatin ta kashe kudi wajen gyara asibitocin gwamnati

- Gwamnatin ta gyara makarantun gwamnati guda biyar a garuruwan jihar

Gwamnatin jihar Yobe ta kaddamar da anfani da kudi Naira miliyan 777 don anfani da su wajen siyo ingatattun kayan aikin asibiti da za a saka a asibitocin gwamnati na Gashua da Potiskum.

Gwamnatin Yobe zata kashe Naira miliyan 770 wajen samar da ingatattun kayan aikin asibiti da makarantu

Gwamnatin Yobe zata kashe Naira miliyan 770 wajen samar da ingatattun kayan aikin asibiti da makarantu

Alhaji Mala Musti, kwamishinan yada labarai na jihar ne ya shaida hakan a karshen taron da suka yi da manyan ‘yan majalisar jihar a Damaturu.

A shekarar 2016 ne kungiyar ta amince da anfani da Naira biliyan 1.8 wajen gyara asibitocin gwamnatin jihar.

Burin gwamnatin ne ta ga ta samar wa da mutanen jihar Yobe ingatattun asibitoci domin anfanin su.

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa har yanzu farashin kayan abinci basu sakko ba

A taron Alhaji Musti ya kara shaidawa gwamnatin ta amince da anfani da Naira miliyan 98 wajen siyo kayan aikin kimiyya na gwaje-gwaje a makarantun da aka gyara don dalibai su sami ingataccen ilimi.

Ya shaida yadda gwamnatin ta gyara wasu makarantun gwamnati guda biyar na garin Nangere, Fika, Yunusari, da Nguru don dalibai su sami ilimi mai anfani.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyauta

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyauta

Gwarzon ‘Yan wasan kwaikwayo Ali Nuhu na shirin lashe kyautar 2017
NAIJ.com
Mailfire view pixel