Kiranyen Dino Melaye: Umarnin kotu mu ke jira – Shugaban INEC

Kiranyen Dino Melaye: Umarnin kotu mu ke jira – Shugaban INEC

- Hukumar INEC ta bayyana cewa umurnin kotu take jira don yiwa Sanata Dino Melaye kiranye

- Shugaban Hukumar INEC, Mahmud Yakubu ne ya sanar da haka a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai

- Dino na ta kokarin ganin ba'ayi nasarar yi masa kiranye ba kamar yadda al'umman mazabarsa suka nema

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC), ta sanar cewa umurni kawai take jira daga kotu domin ta san abun yi na gaba a kan yunkurin yiwa Sanata Dino Melaye Kiranye.

Shugaban Hukumar INEC, Mahmud Yakubu ne ya sanar da haka a ranar Talata, 3 ga watan Oktoba lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a babban birnin tarayyaAbuja.

A halin da ake ciki dai a yanzu Melaye ya kai-gwauro-kai-mari wajen kokarin ganin ba’a yi nasarar yi masa kiranyen da al’umman mazabar ta sa daga Jihar Kogi ta Yamma ke kokarin yi masa ba.

KU KARANTA KUMA: Wani jigo a jam’iyyar APC, Mustapha ya tona asirin asalin makiyan Buhari

A ranar 23 ga watan Yuni da ta gabata ne suka aika da takardun korafe-korafe tare da neman yi ma sanatan nasu kiranye ga hukumar zabe.

Yayin da shi kuma Dino ya garzaya zuwa gaban babbar kotun tarayya, da nufin ta dakatar da yi masa kiranyen.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Canji: Hotunan ƙarin sabbin taragon jirgin kasa na Abuja-Kaduna sun iso Najeriya

Canji: Hotunan ƙarin sabbin taragon jirgin kasa na Abuja-Kaduna sun iso Najeriya

Canji: Hotunan ƙarin sabbin taragon jirgin kasa na Abuja-Kaduna sun iso Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel