Jam'iyyar APC na zargin Ali Modu da yi mata sojan gona

Jam'iyyar APC na zargin Ali Modu da yi mata sojan gona

- Jam'iyyar APC reshen jihar Borno na zargin Ali Modu da yi mata sojan gona

- Jam'iyyar ta ce yana ikirarin shine mataimakin shugaban jam'iyyar yankin arewa maso gabas

- Sun zarge shi da yunkurin karbar ragamar jam'iyyar ta barauniyar hanya

Jam'iyyar APC reshen jihar Borno ta zargi tsohon hambararren shugaban jam'iyyar PDP, Ali Modu Sheriff, da yiwa jam'iyyar sojan gona tare da kokarin karbar ragamar jam'iyyar ta barauniyar hanya.

Jam'iyyar APC na zargin Ali Modu da yi mata sojan gona

Jam'iyyar APC na zargin Ali Modu da yi mata sojan gona

Jam'iyyar tayi wannan ikirari ne a wata takarda da sakataren yada labarai na jam'iyyar APC a Jihar Borno, Makinta Zarami, ya aike ga kafafen yada labarai. Jam'iyyar ta bayyana cewar Ali Modu na ikirarin shi ne mataimakin Shugaban jam'iyyar APC na yankin arewa maso gabas, sannan kuma yana nuna cewar a mataki daya yake da dakarun jam'iyyar irin su, Bola Tinubu, Obonnayya Onu, da Atiku Abubakar.

DUBA WANNAN: Kora da hali? Ministoci sun kasa ganin shugaban kasa

Jam'iyyar ta kara zargar Ali Modu da kitsa rahoton cewar jam'iyyar ta APC na zawarcin sa bayan da kotu ta hambarar da shi daga shugabancin jam'iyyar PDP. Jam'iyyar APC ta ce Ali Modu na jawo mata abin kunya a saboda haka ta ce ya zama dole ta fito ta yi magana don bata tsoron sa.

Sakataren yada labaran jam'iyyar APC ya ce Ali Modu na amfani da kafafen sada zumunta wajen yin sojan gona ta hanyar yada cewar jam'iyyar APC ta nada shi mataimakin Shugaban jam'iyyar na yankin arewa maso gabas.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000
NAIJ.com
Mailfire view pixel