Sirrika 12 na amfani da bawon lemun zaki ga rayuwar dan Adam

Sirrika 12 na amfani da bawon lemun zaki ga rayuwar dan Adam

Dan itace na lemun zaki yana da kunshe da sunadarin Vitamin C wanda yake da matukar amfani ga lafiya da kuma fatar jikin dan Adam. Naij.com ta kawo muku rahoton cewa, binciken masana kiwon lafiya na fannin kanyan ciyaciye da na sha sun bayyana cewa, mafi yawan amfanin lemun zaki yana kunshe ne a cikin fatar bayan sa.

1. Ana sanya bawon lemu a rana ya bushe domin yin amfani da dakakken garinsa wajen dakawa da sabulun wanka domin ganin fatar dan Adam cin yalwar lafiya.

2. Ga masu bukatar jin kamshi a cikin gidajensu, ana tafasa busasshiyar fatar lemu domin kamsasa gida.

3. Ga masu kurajen fuska, bawon lemu wata dama ce ta hanyar goga sa a jikin fuska domin samun waraka daga kurajen fuska.

Sirrikan bawon lemun zaki

Sirrikan bawon lemun zaki

4. Da yawan mutane da ba su fiye son amfani da igiyar leko ba, su kan busar da bawon lemu domin sanya shi saman garwashi, wanda wannan hayaki ke korar sauro tare da kamsasa daki.

5. An kwaba garin bawon lemu domin shafawa a gashi a kwana dashi, wannan dabarar ta na taimakawa wajen korar amosanin ka da kuma karyewar gasu tare da tsaftace su.

6. An jika bawon lemu a cikin ruwa sannan a kurbe, wanda hakan yake kawar da cutar kwarnafi da kuma tashin zuciya.

7. Yin amfani da bawon lemu a matsayin abin ci ya kan taimaka wajen kawar da cutar asma.

KARANTA KUMA: Gwamna mai makamanciyar bajinta ta Buhari yake bukata - Obiano

8. Sakamakon amfani da kamshi na bawon lemu idan an tafasa shi, yan da matukar amfani ga ma'abota shan shayi.

9. Bawon lemu bai tsaya iya waraka ga cutar asma kadai ba, domin kuwa yana taimakawa masu hawan jini wajen tabbatar da koshin lafiyar zuciya.

10. Shakar kamshin bawon lemu ya na kawar da ciwon kai, tare da kawar da damuwa.

11. Ga masu fama da warin baki, tattauna bawon lemu a cikin baki yana kawar da wannan wari na baki.

12. Amfani da bawon lemu a wajen tafasa ruwan shayi yana kawar da nauyin jiki sakamakon sunadarin fiber da yake kunshe da shi.

Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel