Kungiyar kwadago ta zargi gwamnati da jan kafa akan maganar karin albashi

Kungiyar kwadago ta zargi gwamnati da jan kafa akan maganar karin albashi

- Har yanzu gwamnati ta yi shiru game da karin albashin ma'aikata

- Kungiyar kwadago ta shaida hakurin ta ya kai bango

- Wasu jihohin basa biyan ma'aikata albashi duk da kudin ba wani abin azo a gani bane

Mataimakin shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya, Mista Solomon Adelegan ya sanar da cewa gwamnatin tarayya na jan kafa wajen karin albashin ma’aikata bayan sun dade da fitar da sanarwar cewa ya kamata a karawa ma'aikata albashi.

A tsarin karin albashi, duk bayan shekara biyar gwamnati zata sake fitar da sabon tsarin biyan albashin ma’aikata, amma har yanzu shiru gwamnati batace komai ba game da karin albashin.

Kungiyar kwadago ta zargi gwamnati da jan kafa akan maganar karin albashi

Kungiyar kwadago ta zargi gwamnati da jan kafa akan maganar karin albashi

Shekara bakwai Kenan amma har yanzu gwamnati batace komai ba duk da ciyaman din kungiyar, Ayuba Wabba ya fitar da takardar neman karin albashin. Kungiyar ta shaidawa gwamnati cewa hakurin su ya kare, domin kuwa akwai abubuwa da yawa da zasu iya yi.

Ma’aikata sun gaji da zaman ku-ku-ku, suna iya bakin kokarin su ne wajen aiki duk da halin da suke ciki, don haka ba lalllai su yi aikin da ake so ba.

Kungiyar ta yi kira ga gwamnati da tayi saurin daukan mataki akan albashin su ganin yadda matsin tattalin arzikin da kasa take ciki. Wasu ma’aikatan kuwa da yawa a wasu jihohin ma ba a biyan su albashi duk da albashin ba wani abin a zo a gani bane.

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa za a yafewa Dangote biyan harajin shekara 3

Gwamnati tana kukan ana cikin matsin tattalin arziki bata iya biyan albashi amma su suke tuka motocin alfarma. Kungiyar ta yi kira ga gwamnati cewar in dai bata karawa ma’aikata albashi ba to kuwa lallai zata kira ma’aikatan Najeriya su fito don su nemi hakkin su.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel