Labara mai daɗi: Manoman shinkafa zasu karya farashinsa warwas!

Labara mai daɗi: Manoman shinkafa zasu karya farashinsa warwas!

Kungiyar manoman shinkafa ta kasa, RIFAN ta dau alwashin karairaya farashin buhun shinkafa kilo 50 zuwa naira N6000, muddin gwamnati ta basu kayan aikin da suke bukata.

Majiyar NAIJ.com, jaridar Tribune ta ruwaito shugaban kungiyar Aminu Goronyo yana fadin haka bayan wata ganawa da aka yi tsakanin shuwagabannin kungiyar da ministan harkokin noma, inda yace muddin ta taka rawar daya kama ce ta, za’a cimma bukata.

KU KARANTA: Jagwal: Wani mutumi ya ɗauki alhakin yi ma Uwa da Ýarta ciki a lokaci ɗaya

A yanzu farashin buhun shinkafa kilo 50 ya kai N18,000, amma bayan ganawar da suka yi da ministan, manoman sun yi alkawarin karya farashin shinkafar zuwa N16,000, sa’annan zuwa N13,500.

Labara mai daɗi: Manoman shinkafa zasu karya farashinsa warwas!

Gonar shinkafa

“A yanzu haka mun tattauna da masu sarrafa shinkafa, saboda muna sa ran samun girbi mai kyau, don haka muna sa ran farashin zai kara karyewa.” Inji Goronyo

Shugaban ya cigaba da fadin “Muna sa ran farashin kilo 50 zai karye zuwa N6,000 a cikin yan watannin kadan, muddin minista ya cika alkawarinsa na ganin sun rage kudin sarrafa shinkafa.”

Haka zalika shima shugaban kungiyar masu sarrafa shinkafa yace manufar ganawarsu da ministan shine su sanar da shi bukatar su ta karya farashin shinkafa zuwa N13,500.

Dayake nasa jawabin, ministan noma Audu Ogbeh yace idan har aka karya shinkafar zuwa N13,500, za’a rage samun masu yin fasa kaurin shinkafar, don haka yace zasu taimaka ma manoman shinkafar ta hanyar siyo musu na’u’rorin sarrafa shinkafa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin

Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin

Hukumar 'yan sanda ta kori wani jami'inta wanda ya harbi direba akan cin hancin naira hamsin
NAIJ.com
Mailfire view pixel