Boko Haram: Za mu kawar da Boko Haram kwanan nan – Inji babban hafsan soja

Boko Haram: Za mu kawar da Boko Haram kwanan nan – Inji babban hafsan soja

- Babban Hafsan Soja ya ce rundunar sojan Najeriya za su kawar da 'yan Boko Haram a cikin gajeren lokaci

- Buratai ya ce, sojojin Najeriya sun rage ayyukan 'yan ta'adda a yankin arewa maso gabas

- Buratai ya bayyana cewa rundunar soja za su share ‘yan kunar bakin wake gaba daya a fadin Najeriya

Babban Hafsan Soja (COAS), Leftanal Janar Tukur Buratai, ya sake jaddada kudurin rundunar sojan Najeriya wajen kawar da 'yan kuna bakin wake Boko Haram a cikin gajeren lokaci.

Bugu da kari, Buratai ya ce, sojojin Najeriya sun rage ayyukan 'yan ta'addan a yankin arewa maso gabashin kasar.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, babban hafsa sojan ya sanar da wannan a lokacin bude taron manema labarai wanda ofishin jami’in hulda da jama’a na sjo ta shirya a Abuja, ya yi kira ga dukkan 'yan Najeriya su hada kai da sojoji domin cin nasara a kan kungiyar Boko Haram, cewa yaki da 'yan ta'adda ba aikin soja kadai bane.

Boko Haram: Za mu kawar da Boko Haram kwanan nan – Inji babban hafsan soja

Babban Hafsan Soja (COAS), Leftanal Janar Tukur Buratai

Buratai ya ce: "Za mu ci gaba da durkushe ‘yan ta’adda har sai mun share su gaba daya a fadin Najeriya musanmman yankin arewa maso gabas’’.

KU KARANTA: Shugaban hafsan soji ya kaddamar da gagarumin aiki a Maiduguri (hotuna)

Babban hafsan ya ci gaba da cewa burin su shine cimma wannan a cikin mafi kankanin lokaci.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dalilin da yasa kotu ta sake kekashewa akan bayar da belin Maryam Sanda

Dalilin da yasa kotu ta sake kekashewa akan bayar da belin Maryam Sanda

Dalilin da yasa kotu ta sake kekashewa akan bayar da belin Maryam Sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel