APC ba ta cancanci zama jam'iyya ba - Buba Galadima

APC ba ta cancanci zama jam'iyya ba - Buba Galadima

Sanannen jigon nan na jam'iyyar APC dake mulki a Najeriya watau Injiniya Buba Galadima ya bayyana matukar damuwar sa a bisa yadda jam'iyyar ta kasa gudanar da taron kwamitinta amintattun ta kusan shekaru uku kenan bayan kafuwarta.

A cewar sa: "APC ba ta cancanci zama jam'iyya ba kwata-kwata. Ya cigaba da cewa tsarin mulkin jam'iyyar dai ya tanadi cewa kwamitin amintattu da kwamitin gudanarwa na kasa da kwamitin wakilan tsara manufofin jam'iyyar na kasa dole ne suyi yi taro akalla sau hudu a shekara.

APC ba ta cancanci zama jam'iyya ba - Buba Galadima

APC ba ta cancanci zama jam'iyya ba - Buba Galadima

KU KARANTA: Dan Boko Haram da aka kama a Ondo ya fara aman bayanai

NAIJ.com dai ta samu cewa Injiniya Buba Galadima ya kara da cewa har yanzu jam'iyyar ba ta taba waiwayar manyan jiga-jigan da suka kafa ta ba tun bayan nasarar da aka samu a zaben 2015.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a kanan baya ma dai shahararren dan siyasar ya bayyana yadda shugaba Buhari yayi watsi da lamarin sa inda kuma ya sha alwashin cewa ba zai taba rokon sa ba domin yayi aiki a cikin gwamnatin sa ba.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel