Yadda rundunar sojin sama ta Najeriya tayi sama-da-fadi da Naira Biliyan 22

Yadda rundunar sojin sama ta Najeriya tayi sama-da-fadi da Naira Biliyan 22

Wani matashi mai suna Tosin Owobo da yake matsayin mai shaida kan wani bincike da hukumar dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa watau EFCC ya shaidawa alkalin babbar kotun tarayya a Legas yadda rundunar sojin samar Najeriya tayi sama-da-fadi da Naira Biliyan 21.

Matashin ya bayyana hakan ne a lokacin da yake bayar da ba'asi a gaban kotun yayin shari'ar da ake ci gaba da yi na tsohon hafsan rundunar sojin Air vice Marshall Adesola Amosu mai ritaya hade da wasu sauran mutane 10.

Yadda rundunar sojin sama ta Najeriya tayi sama-da-fadi da Naira Biliyan 22

Yadda rundunar sojin sama ta Najeriya tayi sama-da-fadi da Naira Biliyan 22

KU KARANTA: Asibitin fadar shugaban kasa zai koma na kudi

NAIJ.com dai ta samu cewa an dai kama Air vice Marshall Adesola Amosu mai ritaya a 29 ga watan Juni shekarar da ta gabata tare da Air Vice Marshal Jacob Bola Adigun, Air Commodore Gbadebo Owodunni Olugbenga da kuma wakillan wasu kamfunna 8.

Shi dai shaidar ya bayyana cewa wata ma'aikaciyar bankin Zenith ne mai suna uwar gidan Funke Osisanmi ce dai tayi ta cire kudaden daga cikin asusun rundunar bayan ta samu umurni daga hafsan sojin rundunar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hotuna: Shugaba Buhari ya dawo daga kasar Faransa inda ya halarci taron shugabanin kasashen duniya a kan dumaman yanayi

Hotuna: Shugaba Buhari ya dawo daga kasar Faransa inda ya halarci taron shugabanin kasashen duniya a kan dumaman yanayi

Hotuna: Shugaba Buhari ya dawo daga kasar Faransa inda ya halarci taro a kan dumaman yanayi
NAIJ.com
Mailfire view pixel