Majalissar dattawa za ta binciki shugaban NNPC, Baru akan zargin da Kachikwu yayi masa

Majalissar dattawa za ta binciki shugaban NNPC, Baru akan zargin da Kachikwu yayi masa

- Shugaban majalissar dattawa ya ba da umarnin kafa kwamtin da za ta bincike al'amarin NNPC

- Senata Kabiru Marafa yayi kira da majalissar ta binciki matsalar da ke tsakanin Maikanti Baru da Ibe Kachikwu

Majalissar datttawa a ranar Laraba ta fara yunkurin binciken hukumar NNPC akan zargin da ake ma ta na cin hanci da rashawa.

Wannan kudurin ya zo ne daga shugaban kwamitin bincike Senata Anyanwu Samuel.

Majalissar za ta bincike kamfanin Duke Oil, wanda aka bata lasisin aiki a Najeriya amma ba ta biyan haraji.

Majalissar dattawa za ta binciki shugaban NNPC, Baru akan zargin da Kachikwu yayi masa

Majalissar dattawa za ta binciki shugaban NNPC, Baru akan zargin da Kachikwu yayi masa

Senata Kabiru, Marafa yayi kira da kwamtin da ta gaggauta binciken al’amarin dan kawo sakamako a kan lokaci.

KU KARANTA : Charlyboy da kungiyar sa sun maka yan sanda a kotu akan cin mutuncin su da suka yi da neman diyar naira miliyan N500m

Bayan haka ya ja hankalin majalissar akan rikicin dake tsakanin karamin ministar harkan mai Dakta Ibe Kachikwu da daraektan hukumar NNPC, Mai kanti Baru.

Marafa ya ce majalissar ta binciki zargin da ministar yayi wa Maikanti Baru a cikin wasikar da ya rubuta wa shugaban kasa saboda magance matsalar kafin ya wuce gona da iri.

Shugaban majalisar dattawa, Dakta Bukola Saraki, ya ba da umarnin kafa kwamtin da za ta binciki yadda ake gudanar da abubuwa a NNPC.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen

Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen

Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen
NAIJ.com
Mailfire view pixel