Kora da hali? Ministoci sun kasa ganin shugaban kasa

Kora da hali? Ministoci sun kasa ganin shugaban kasa

- Wasu minitoci sun dau wajen wata shida suna neman ganawa da Buhari amma abin ya ci tura

- Wasikar da Ibe Kachikwu ya aikawa Buhari ta fada hannun bainar jama'a

- Ana kira ga Buhari da duba lamarin

Ministoci sun koka da hana su ganin Shugaba Buhari da na kusa da shi ke yi. Wannan ya fito fili ne da wata wasikar Ministan Man Fetur, Ibe Kachikwu, ya aikawa Buhari ta yi batan kai ta fada hannun bainar jama'a.

Kora da hali? Ministoci sun kasa ganin shugaban kasa

Kora da hali? Ministoci sun kasa ganin shugaban kasa Hoto daga The Cable

A cikin wasikar Kachikwu ya soki sabon shugaban NNPC, Maikanti Baru, kuma ya koka da cewa ya kasa ganin shugaban kasar tun lokacin da suka taro shi a filin jirgi bayan dawowar shi daga jinya a Landan.

Kachikwu ya kai wa Buhari ziyara a lokacin da yake jinya amma babu tabbacin ya samu ganin shi. Saboda haka ana kyautata zaton ya kusa wata shida rabon shi da ya gana da uban-gidan sa.

Ba Kachikwu kadai ba, a bayan taron da aka yi da bankin duniya (World Bank) da kuma kungiyar masu bawa kasashe bashi (IMF), ministocin da suka wakilci Najeriya a kan tsararrakin ci gaban da ake so a zartar sun fayyace duk abubuwan da suke bukata shugaban kasa ya sa hannu don a fara zartar da aiki. Amma da suka dawo gida, har yau ba su sami gain shi ba.

DUBA WANNAN: Za a mayar da asibitin fadar shugaban kasa na kudi

Bayan wannan kuma, cacar bakin da Isaac Adewole, ministan lafiya, da kuma Usman Yusuf, shugaban ishorar lafiya (NHIS), inda Adewole ya kori Yusuf daga aiki. Shi kuma Yusuf ya ce shugaban kasa ne kawai zai iya sallamar sa. Shi kuma Adewole har yau ya kasa ganawa da shugaban kasa.

Ya kamata Shugaba Buhari ya duba wannan lamari, ya bashi muhimmanci don kasa ta samu ci gaba na musamman.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, a tuntube mu a:

labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen

Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen

Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen
NAIJ.com
Mailfire view pixel