Karfaffan direban mota ya bazar da wani Fasinja, ya zubar masa hakora

Karfaffan direban mota ya bazar da wani Fasinja, ya zubar masa hakora

- Rikici a tasha tsakanin Direba da Fasinja yayi sanadiyyar yima juna jini da majina

- Kotu ta bada belin direban akan naira 25,000

Wani matashin Direba Jimoh Rafiu ya zubar ma wani fasinjansa hakora bayan ya jibjibga masa naushi a baki sanadiyyar takaddama akan kudi daya shiga tsakaninsu.

Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a ranar 14 ga watan Satumba, a tashar mota ta Salolo dake kan titin Legas zuwa Abekuta, yayin da direban yaki mayar ma fasinjar kudinsa yayin da iskar tayar motarsa ta sace, kamar yadda dansanda mai kara ya shaida ma kotu.

KU KARANTA: Dala biliyan 30: Buhari ya baiwa gwmanan jihar Jigawa, gagarumar aiki

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito dansanda mai kara, Sufeta Victor Eruada yana shaida ma kotu a cewa Direba Jimoh ya farfasa ma Fasinja Abraham Kunle baki kawai don ya bukaci ya bashi kudinsa, inda yace hakan ya saba ma sashi na 171 da 172 na dokokin jihar Legas.

Karfaffan direban mota ya bazar da wani Fasinja, ya zubar masa hakora

Direban mota

Sai dai wanda ake zargin ya musanta aikata laifin, don haka alkalin kotun ya bada belin Direban akan N25,000 tare da mutane biyu da zasu tsaya masa, sa’annan ya dage sauraron karar zuwa 20 ga watan Oktoba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

We need to understand the Biafra objective, NAIJ.com TV

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel