Dubban magoya bayan Jam’iyyar APC sun Koma PDP a jihar Kogi

Dubban magoya bayan Jam’iyyar APC sun Koma PDP a jihar Kogi

- Dubban yan APC sun sauya sheka zuwa PDP a jihar Kogi

- Tsohon mataimakin shugaban karamar hukumar Mopamuro ne ya jagoranci masu sauya shekar

- Sun zargi jam’iyyar da rashin tsinana wa al’ummar jihar komai

Dubban masu goyon bayan Jam’iyyar APC sun sauya sheka zuwa daga jam’iiar su zuwa jam’iyyar PDP a jihar Kogi.

Tsohon mataimakin shugaban karamara hukumar Mopamuro, Oyebode Makind ne ya jagoranci masu sauya shekar.

A cewar tsohon shugaban yace sun sauya sheka ne saboda da lura da sukayi da cewa jam’iyyar bata iya yi wa mutanen jihar Komai ba zuwa yanzu kuma ya ce zasu tabbatar da ganin cewa PDP ta samu nasara a jihar.

KU KARANTA KUMA: Jami’an yan sanda sun tisa keyar wasu da ake zargin yan fashi ne a Benue

A baya NAIJ.com ta tattaro cewa tsohon alkalin alkalai kuma ministan shari’a a jamhuriyar Najeriya ta biyu, Cif Richard Akinjide (SAN), ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari kan sake takara a 2019 inda ya bayyana yunkurin haka a matsayin tatsuniya.

A hira da Cif Akinyemi yayi da jaridar Punch, yace tunda Buhari ya samu abunda yake so, ya tafi ya hutu yayinda sauran yan siyasa na hakika zasu karbi shugabancin kasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel