Biyafara : Kungiyar matasan Arewa ta caccaki IPOB akan sukar da su ka yi wa Orji Uzo Kalu game da bacewar Nnamdi Kanu

Biyafara : Kungiyar matasan Arewa ta caccaki IPOB akan sukar da su ka yi wa Orji Uzo Kalu game da bacewar Nnamdi Kanu

- Kungiyar matasan Arewa ta caccaki IPOB

- Shugaban kungiyar ya ce IPOB ba sa son gaskiya

- Yerima yaji mamakin yadda yan kingiyar IPOB suke sukar Kalu duk da kokarin da yake mu su

Kungiyar matasan Arewa (AYLF) a ranar Laraba ta caccaki kungiyar yan asalin Biyafara IPOB akan sukar da suka yi wa tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Kalu akan magananun da yayi game da bacewar shugaban kungiyar, Nnamdi Kanu.

A karshen makon da ya gabata ne Kalu ya ce shugaban IPOB ya tsere daga Najeriya zuwa Landan ta kasar Malaysia.

Wannan shine maganar da ya yi wa kungiyar IPOB zafi, yasa suka fito suka fara sukar shi.

Biyafara : Kungiyar matasan Arewa ta caccaki IPOB akan sukar da su ka yi wa Orji Uzo Kalu game da bacewar Nnamdi Kanu

Biyafara : Kungiyar matasan Arewa ta caccaki IPOB akan sukar da su ka yi wa Orji Uzo Kalu game da bacewar Nnamdi Kanu

ACF ta mayar da martani ga suka da IPOB su ka ma tsohon gwamnan, da cewa yan kungiyar ba su da tunani da sanin abun da yakamata, kuma ba sa son gaskiya.

KU KARANTA : Yan sanda sun kama diribobin taksi na Uber 2 da zargi yiwa fasinja sata

Shugaban kungiyar matasan Arewa, Alhaji Shettima Yerima yayi mamakin yadda yan kungiyar IPOB suke zagin Orji Kalu, bayan shi ke neman sassanci tsakanin su da gwamnati.

A jawabin da Yerima yayi yace, “ Mutum kamar Kalu wanda kullun yana kan hanyar zuwa Arewa dan nemar sulhu saboda kare rayukan mutanen sa a yankin, ya na bukatar yabo ne ba zagi ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa
NAIJ.com
Mailfire view pixel