Zai zama babban tatsuniya idan Buhari ya nemi tsayawa takara a 2019 - Akinjide

Zai zama babban tatsuniya idan Buhari ya nemi tsayawa takara a 2019 - Akinjide

- Tsohon alkalin alkalai na Najeriya, , Cif Richard Akinjide ya shawarci Buhari da kar ya sake tsayawa takara a 2019

- Ya ce ya kamata shugaban kasar ya huta ya kuma kyale ainihin yan siyasa su karbi shugabanci a 2019

- Cif Akinjide har ila yau ya lura cewa ba'a bukatar fafatukar kafa kasar Biyafara

Tsohon alkalin alkalai kuma ministan shari’a a jamhuriyar Najeriya ta biyu, Cif Richard Akinjide (SAN), ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari kan sake takara a 2019 inda ya bayyana yunkurin haka a matsayin tatsuniya.

A hira da Cif Akinyemi yayi da jaridar Punch, yace tunda Buhari ya samu abunda yake so, ya tafi ya hutu yayinda sauran yan siyasa na hakika zasu karbi shugabancin kasa.

NAIJ.com ta tattaro cewa a lokacin da aka bukaci ya bayyana ra’ayinsa kan nasarorin Buhari tun 2015, Cif Akinjide ya ce: Tsammanin ku yayi iri daya da nawa. Da na fi son cewa tunda Buhari ya samu abunda yake so, ya tafi ya huta sannan sauran yan siyasan ainihi su karbi mulki

Amman mutane basu saurari gaskiya ba; rabin gaskiya suke son ji hade da rabin karya. Yayinda yake amshi ga masu kira ga Buhari da ya sake takara a 2019, ya ce: “Na yi dariya kan al’amarin. Idan har ya sake tsayawa takara, zai kasance babban ba'a.”

KU KARANTA KUMA: Jami’an yan sanda sun tisa keyar wasu da ake zargin yan fashi ne a Benue

Kan fafatukar kungiyar IPOB, Chief Akinjide ya ce ba zai goyi bayan hargitsa Najeriya ba

A halin da ake ciki, NAIJ.com ta rahoto a baya cewa an rantsar da sabuwar ofishin kudu maso yamma na yakin neman zaben shugaba Muhammadu Buhari a 2019 wacce ta dauki alkawarin tabbatar da cewan an sake zaban shugaban.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel