Biyafara ruhi ne da bindigogi da sauran makamai bazasu iya kashe ta ba – Fasto Chris Okafor

Biyafara ruhi ne da bindigogi da sauran makamai bazasu iya kashe ta ba – Fasto Chris Okafor

- Wannan Faston mazaunin Lagas Fasto Chris Okafor yace babu mai iya kashe fafutukar Biyafara ta hanyar amfani da dole

- Fasto Okafor ya kuma bayyana cewa duk wanda ke tunanin zai iya aikata hakan toh wawa ne

- Fasto Okafor yayi ikirarin cewa Biyafara ruhi ne da bindigogi bazasu iya kashe ta ba

Fasto Chris Okafor, shugaban cocin Mountain of Liberation and Miracle Ministry, ya bayyana cewa Biyafara wata ruhi ce da baza’a iya kashe ta da bindigogi ba, makamashi, ko kuma bam.

Okafor ya kuma bayyana cewa duk wanda ke tunanin zai iya aikata hakan toh wawa ne.

Rahotanni sun kawo cewa Fasto Okafor ya bayyana hakan ne yayinda yake taya Najeriya murna a ranar bikin yancin kanta.

KU KARANTA KUMA: Koriya ta Arewa ta jefa Japan cikin Zullumi

A cewar sa ya kamata gwamnati ta koyi zama don sassanci, cewa lokaci ba ya baci wajen neman sassanci.

Faston yace shi baya kira ga rabewar Najeriya amma idan har Najeriya bata daidaita ayyukanta ba, abubuwa na iya tabarbarewa kuma babu wani yunkuri da zai hana hakan. Ya kum bukaci masu bauta da suyi ma Najeriya addu’an zaman lafiya da hadin kai.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dalilin da yasa kotu ta sake kekashewa akan bayar da belin Maryam Sanda

Dalilin da yasa kotu ta sake kekashewa akan bayar da belin Maryam Sanda

Dalilin da yasa kotu ta sake kekashewa akan bayar da belin Maryam Sanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel