Kalaman Oyegun akan rashin daukan wasu yankuna da muhimmaci abun takaici ne – Reveran Tunde Adeyeye

Kalaman Oyegun akan rashin daukan wasu yankuna da muhimmaci abun takaici ne – Reveran Tunde Adeyeye

- Shugaban kungiyar majalisar kiristoci yayi wa Oyegun raddi

- Adeyeye ya ce sauya fasalin Najeriya ka dai zai kawo karshen matsalolin Najeriya

- Tunde Adeyeye yace yana ganin mutuncin Oyegun amma yayi takaicin maganar da yayi

Shugaban kungiyar majalissar kristocin Najeriya (CCN) Rev. Tunde Adeleye, yayi tsokaci akan maganar da shugaban jam’iyyar APC, Cif John Odigie Oyegun na cewa mutanen yankin kudu maso gabas ba su da izinin cewa gwamnatin APC ta share su saboda bas a goyon bayan ta.

Rev Adeleye ya fadi haka ne lokacin da yake zantawa da manema labarai Calabar, ‘ya ce yayi takaici da ya ji maganar da Oyegun yayi, inda ya ce idan ba sa son gwamnati ta share su, su shiga jam’iyyar APC. Wannan maganar ba a jarida kadai na karanta ba, naji shi da kunne na a talabajin.

Kalaman Oyegun akan rashin daukan wasu yankuna da muhimmaci abun takaici ne – Reveran Tunde Adeyeye

Kalaman Oyegun akan rashin daukan wasu yankuna da muhimmaci abun takaici ne – Reveran Tunde Adeyeye

“Mutane suna korafin cewa gwamnati ta share su, wani kuma yana cewa idan ba sa son a cigaba da share su, su shiga APC, wannan kalma ta yi muni da yawa. Oyegun mutum ne da nake ganin mutuncin sa sosai.

KU KARANTA : Yan sanda sun kama diribobin taksi na Uber 2 da zargi yiwa fasinja sata

"Ban taba tunanin irin wannan maganar zai iya fitowa daga bakin sa ba. Shi yasa nayi takaici sosai."

Mallamin addini krista, yace sauya fasalin kasar kadai zai magance matsalolin da kasar ke fuskanata.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa
NAIJ.com
Mailfire view pixel