Tashin Dala: CBN zai saki makudan Daloli

Tashin Dala: CBN zai saki makudan Daloli

- Babban bankin Najeriya CBN zai saki Miliyoyin Daloli

- Bankin na CBN ya dade yana dafawa Naira a kasuwa

- Babban Jami’in bankin ya bayyana haka a makon nan

Yanzu mu ke samun labari daga Jaridar The Cable cewa babban bankin Najeriya zai saki miliyoyin Daloli domin a samu sauki a kasuwa.

Tashin Dala: CBN zai saki makudan Daloli

Gwamnan Bankin CBN Emefiele

A halin yanzu ma dai babban bankin Najeriya na CBN zai saki Dala Miliyan 100 ga manyan ‘Yan kasuwa yayin da aka ware wasu Dala Miliyan 50 ga kananan ‘yan kasuwar kasar watau SME. A baya dai bankin ya ware Dala Miliyan 45 ga masu fita kasar waje.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya jagoranci taron Majalisa

Babban Jami’in bankin Isaac Okorafor ya tabbatar da wannan bayani inda yace bankin zai cigaba da taimakawa Nairar a kasuwa. A makon jiya dai bankin na CBN ya ware $698.5 a kasuwa wanda ya sa Naira ta kara daraja kan Dalar Amurka wanda yanzu ke kan N364.

Dazu kun ji cewa Ministar kudi na kasar nan a wani zama da tayi da Ministan kasafi tace abin da aka samu na kudi bai wuce Tiriliyan daya da rabi ba don haka ba za a iya aiwatar da ayyukan da ke cikin kasafin kudin bana ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel