Koriya ta Arewa ta jefa Japan cikin Zullumi

Koriya ta Arewa ta jefa Japan cikin Zullumi

- Koriya ta Arewa ta jefa kasar Japan cikin fargaba

- Hakan ya faru ne sakamakon fitar da sanarwar da tayi na cewa imma dai Japan ta taina matsa mata ko kuma ita ta harba mata Nukiliya

Koriya ta Arewa ta jefa kasar Japan cikin fargaba, hakan ya faru ne sakamakon fitar da sanarwar da tayi na cewa imma dai Japan ta taina matsa mata ko kuma ita ta harba mata Nukiliya

Kamfanin dillancin labaran Koriya ta Arewa (KCNA) ta sanar da cewa, babu wanda zai iya cewa ga takamamman lokacin da rikicin Nukiliyan zai kaure a sashin saboda matsawa da tsangwama da ake ma Koriya ta Arewa. Sai dai idan aka fara wannan rikici toh babu shakka abun zai fara shafar Japan ne inda makaman Nukiliya za su shafe ta gaba daya.

Koriya ta Arewa ta jefa Japan cikin Zullumi

Koriya ta Arewa ta jefa Japan cikin Zullumi

A lokacin taron majalisar Dinkin Duniya karo na 72 wanda aka gabatar a watan Satumba, Firaministan Japan Shinzo Abe ya nuna bukatar a kara karfin takunkumi da hantarar Koriya ta Arewa da ake yi.

KU KARANTA KUMA: Yadda IGP Idris yayi ma jami’a mace ciki, ya kuma aure ta ba bisa tsarin yan sanda ba - Misau

Abe ya ce, dole ne su takura wa Koriya ta Arewa ta bar shirinta na sarrafa Nukiliya. Kuma ba wai ta hanyar tattauna wa ba, a a ta hanyar matsa lamba.

A ranar 15 ga watan Satuumba ne Koriya ta Arewa ta harba makami mai lizami na karshe a yankin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000

Gwamnatin Katsina za ta dauka malaman makarantun firamare 5,000
NAIJ.com
Mailfire view pixel