Femi Fani-Kayode ya kara yin kaca-kaca da Shugaba Buhari

Femi Fani-Kayode ya kara yin kaca-kaca da Shugaba Buhari

- Femi Fani-Kayode ya soki Shugaba Buhari game da rikicin Baru da Kachikwu

- Tsohon Ministan ya bayyana cewa Shugaba Buhari ya dauki ‘Yan kudu bayi

- Ministan mai na kasar ya kai karar Shugaban EFCC wajen Shugaban kasa

Femi Fani-Kayode wani rikakken Dan adawar Gwamnatin Shugaba Buhari ya kara yin kaca-kaca da Shugaban kasar kamar yada Jaridar Daily Post ta rahoto.

Femi Fani-Kayode ya kara yin kaca-kaca da Shugaba Buhari

Tsohon Ministan Najeriya Femi Fani-Kayode

Tsohon Ministan kasar nan Femi Fani-Kayode ya caccaki Shugaban Kasa Muhammadu Buhari saboda takaddamar da ake bugawa tsakanin Shugaban NNPC MaiKanti Baru da Ministan mai n kasar Ibe Emmanuel Kachikwu.

KU KARANTA: Shugaba Buhari yayi abin da ba a taba yi ba

Ministan man fetur na kasar Dr. Ibe Emmanuel Kachikwu ya kai kukan cewa Dr. MaiKanti Baru wanda shi ne Shugaban Kamfanin NNPC na kasa ba ya masa biyayya yadda ya dace a matsayin sa na wanda yake babban sa.

Femi Fani-Kayode ya bayyana a shafin sa na Tuwita cewa Shugaba Buhari ya dauki duk wani Inyamurai tamkar bawa yayin da shi kuma Mai Kanti Baru dan uwan sa ne Bahaushe don haka ka da yayi wani mamaki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Yadda ganawar Shugaba Buhari da Inyamuran APC ta kasance

Yadda ganawar Shugaba Buhari da Inyamuran APC ta kasance

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa
NAIJ.com
Mailfire view pixel