Yadda IGP Idris yayi ma jami’a mace ciki, ya kuma aure ta ba bisa tsarin yan sanda ba - Misau

Yadda IGP Idris yayi ma jami’a mace ciki, ya kuma aure ta ba bisa tsarin yan sanda ba - Misau

Rikicin dake tsakanin sufeto Janar na yan sanda, Ibrahim Idris, da Sanata Isah Hamman Misau, ya fara nisa.

Yayinda dan majalisar ke a gaban majalisar dattawa a ranar Laraba, 4 ga watan Oktoba ya yi zargin cewa shugaban rundunar yan sandan yayi ma wata jami’ar yan sanda ciki sannan kuma a yanzu yana auren ta, wanda a cewar sa hakan ya saba ma tsarin aikin yan sanda.

Sanata Misau ya bayyana cewa tuni an kara ma wannan mata da ake Magana a kanta girma, duk da cewan bata cancanci kaiwa wannan matsayi ba.

A lokacin wannan rahoton ba’a ambaci sunan jami’ar ba yayinda shugaban yan sandan bai maida martini ba tukuna.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya jagoranci zaman majalisa (hotuna,bidiyo)

Sanatan, wanda a yanzu haka yana cikin ganawa da abokan aikinsa, yace ya zama dole a binciki cin hanci da rashawa dake rundunar, karkashin sufeto janar na yanzu, Ibrahim Idris, idan har ana so a dawo da inganci a rundunar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel