Bambarakwai: Uba ya halaka ɗan cikinsa bayan ya yi masa duren maganin ‘kaifin ƙwaƙwalwa’

Bambarakwai: Uba ya halaka ɗan cikinsa bayan ya yi masa duren maganin ‘kaifin ƙwaƙwalwa’

Kamar yadda hausawa ke fadi, idan ajali yazo, ko ba mutuwa sai an je, haka kuma, shi fa tsutsayi baya wuce ranarsa, kwatankwacin haka ne ya faru da wani uba da dansa a jihar Neja.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wani mutumi mai suna Bashir Isah ya gurfana gaban kuliya manta sabo kan laifin kisan kai, inda zake tuhumarsa da kashe yaronsa, dan cikinsa.

KU KARANTA: Majalisar ɗinkin Duniya ta ƙaddamar da shirin samar da abinci na dala miliyan 9 a Kaduna

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito mutumin wanda mazaunin kauyen Ebbo ne, na karamar hukumar Lapai ya kashe dansa, ALiyu Bashir ne bayan da yayi masa duren maganin gargajiya, na kara kaifin kwakwalwa.

Bambarakwai: Uba ya halaka ɗan cikinsa bayan ya yi masa duren maganin ‘kaifin ƙwaƙwalwa’

Kotun

Yansandan garin Lapai sun bayyana cewa mahaifiyar Aliyu, Aisha Bashir ce ta kawo karar mijin nata a ranar 19 ga watan Satumba, inda tace mijinta Isah yayi ma yaron duren maganin ne da nufin ya samu ilimi, inda ba tare da bata lokaci ba, Aliyu yace ga garinku nan.

Dansanda mai kara Emmanuel Danladi ya shaida ma kotu cewa mahaifin yaron ya amsa laifin daya aikata, inda alkalin kotun, Maryam King ta bada umarnin rufe Isah a gidan yari, tare da dage sauraron karar zuwa 26 ga watan Oktoba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

We need to understand the Biafra objective, NAIJ.com TV

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ashe Iran ke baiwa 'yan tawayen Yemen makaman yaki

Ashe Iran ke baiwa 'yan tawayen Yemen makaman yaki

Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen
NAIJ.com
Mailfire view pixel