Kasafin kudin 2017: Gwamnatin Tarayya tace ba ta da kudi

Kasafin kudin 2017: Gwamnatin Tarayya tace ba ta da kudi

- Gwamnatin Tarayya tace ba ta da kudin yin ayyukan da aka kasafta bana

- Yanzu haka an maida ayyukan wannan shekarar zuwa shekara mai zuwa

- A halin yanzu dai wannan shekarar ta kusa karewa ba a kai ga ko in aba

Yanzu mu ke samun labari cewa Gwamnatin Najeriya tace ba ta da kudin yin ayyukan da aka niya a kasafin kudin wannan shekara.

Kasafin kudin 2017: Gwamnatin Tarayya tace ba ta da kudi

Gwamnatin Najeriya tace ba ta da kudi

Dama tun makon jiya Majalisa ta koka da cewa babu abin da aka yi a wannan shekarar inda Darektan Ofishin kasafi ya bayyana cewa ba a samu kudin da aka sa rai ba. Ministar kudi na kasar a wani zama da tayi da Ministan kasafi tace abin da aka samu bai wuce Tiriliyan daya da rabi ba.

KU KARANTA: Ban ba Shugaba Buhari kunya ba Inji El-Rufai

Hakan dai na nufin sama da kashi 60% na ayyukan da aka yi niyyan yi a bana za su koma cikin kasafin kudin shekara mai zuwa. A karshen makon nan ne dai Gwamnati za ta saki makudan Miliyoyi domin wasu ayyuka a fadin kasar. Inji Minista kudi Kemi Adeosun.

Ministan kasafi na Kasar Udo Udoma yace bata lokacin da Majalisa tayi wajen amincewa da kundin kasafin kudin wannan shekarar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel