Dala biliyan 30: Buhari ya baiwa gwmanan jihar Jigawa, gagarumar aiki

Dala biliyan 30: Buhari ya baiwa gwmanan jihar Jigawa, gagarumar aiki

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada gwamna Badaru shugaban kwamitin samar da kudaden shiga

- Ana sa ran kwamitin zata mika rahotonta a farkon watan Nuwamba

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada gwamnan jihar Jigawa shugaban kwamitin samar ma Najeriya dalan Amurka biliyan 30 daga bangaren da basu da alaka da albarkatun man Fetur.

Buhari yayi haka ne a wani mataki na rage dogaro da harkokin man fetur wajen samar ma kasar nan kudaden shiga, domin sake fasalin tattalin arzikin man fetur.

KU KARANTA: Baraka a gwamnatin Buhari: Ministan mai ya kai ƙarar shugaban NNPC

Wannan tsari na gwamnatin shugaba Buhari nada nufin kara dala biliyan 25 ga asusun gwamnati kenan, kari akan dala biliyan 5 da gwamantin ke dasu a yanzu, wanda aka same su daga fannonin da ba na mai ba, musamman samar da kudi ta fitar da kayan gona irinsu Kwakwa, sukari, waken soya, roba, shinkafa, alkama, masara, fatu da ƙiraga,

Dala biliyan 30: Buhari ya baiwa gwmanan jihar Jigawa, gagarumar aiki

Buhari da gwmanan jihar Jigawa

Shugaban hukumar bunkasa kayyakin da ake fitarwa kasashen waje, Segun Awolowo ne ya bayyana haka a karshen taron majalisar tattalin arzikin kasa wanda matamakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranta.

A nan ne aka kafa kwamitin da gwamna Badaru zai jagoranta, wanda ake sa ran zasu zakulo ma gwamnati wasu hanyoyi daban da zasu kara mata kudaden shiga da kimanin dala biliyan 25, daban daga harkar man fetur, kamar yadda jaridar Rariya ta ruwaito.

Kafa wannan kwamiti nada nasaba da manufar gwmanati na samar da dala biliyan 150 a shekaru goma masu zuwa, tare da samar da ayyukan yi gida 500,000, sa’annan da fitar da yan Najeriya miliyan 10 daga kangin talauci, tare da baiwa jihohi daman fitar da kayyakin da take sarrafawa kasashen waje, kamar yadda majiyar NAIJ.com ta ruwaito.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Price of petrol crashes in Nigeria, NAIJ.com TV

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel