Biyafara: Da kamata yayi a tsige Buhari - Ahamba

Biyafara: Da kamata yayi a tsige Buhari - Ahamba

- Mike Ahamba, wani lauyan tsarin mulki, ya zargi majalisar dokoki, da kin yin watsi da aika rundunar yaki ba tare da amincewar su ba

- Ahamba yace yan majalisar suyi bayani kan dalilin da yasa basu tsige dukkan mutanen dake bayan yunkurin ba

- Ya kuma bayyana cewa sashi na 143 na kundin tsarin mulki ya bayyana cewa take dokar tsarin mulki tsigewa ne

Mike Ahamba, wani lauyan tsarin mulki, ya soki majalisar dokoki, da basu tsige shugaban kasa wanda ya tura rundunar yaki aiki ba tare da amincewar su ba.

Rahotanni sun kawo cewa Ahamba yace ayyukan shugabannin kasa Olusegun Obasanjo, Muhammadu Buhari da sauran wadanda suka tura rundunar soji a lokacin zaman lafiya ba tare da amincewar wadanda suka kamara ba ya saba ma kundin tsarin mulki.

KU KARANTA KUMA: Jirgin kasa ya murkushe wasu dalibai yan Indiya uku yayinda suke daukar hoto

Ya bayyana aikin Operation Python Dance II a kudu maso gabas, da kuma amfani da sojoji a lokutan zabe a matsayin yunkuri daya kamata a yi hukunci.

A halin da ake ciki, NAIJ.com ta rahoto cewa Chekwas Okorie, shugaban jam’’iyyar UPP na kasa, yayi ikirarin cewa gwamnati mai ci karkashin shugaba Buhari ne ya raba Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Ashe Iran ke baiwa 'yan tawayen Yemen makaman yaki

Ashe Iran ke baiwa 'yan tawayen Yemen makaman yaki

Ta tabbata' Kasar Iran ke taimakawa 'yan tawayen Kasar Yemen
NAIJ.com
Mailfire view pixel