Baraka a gwamnatin Buhari: Ministan mai ya kai ƙarar shugaban NNPC

Baraka a gwamnatin Buhari: Ministan mai ya kai ƙarar shugaban NNPC

Sahihan bayanai sun fara bayyana dangane da tataburzan dake tsakanin karamin ministan harkokin mai da kuma shugaban hukumar tace man fetur ta kasa, wanda yayi sanadiyar tsatstsamar dangantaka tsakaninsu.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito minista Ibe Kachikwu ya kai karar shugaban NNPC , Maikanti Baru ga shugaban kasa Muhammdu Buhari ta cikin wata wasika daya aike masa.

KU KARANTA: Hadarin jirgin ruwa mai muni yaci mutane 17 yan kasuwa a jihar Kebbi

Baraka a gwamnatin Buhari: Ministan mai ya kai ƙarar shugaban NNPC

Wasikar

Cikin wannan wasikar, minista Kachikwu ya zargi Baru da rashin da’a, ladabi da biyayya a gare shi, tare da bada kwangila ba’a kan tsari ba, inda ta bukaci shugaban kasa ya dauki mataki akan hakan.

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito minista bai jin dadi yadda shugaban NNPC Baru ke zuwa ga shugaban kasa kai tsaye ba tare da ya bi ta wajensa ba, kuma ma yafi ministoci da dama damar ganin shugaban kasar, kuma yana jin maganarsa.

Baraka a gwamnatin Buhari: Ministan mai ya kai ƙarar shugaban NNPC

Wasikar

Minista ya nuna bacin ransa dangane da kwangilar da NNPC ta bayar na aikin bututun iskar gas daga Ajakouta zuwa Kano, wanda zai bi ta Kaduna, ga wani kamfanin China.

Sai dai wata majiya mai sika ta shaid ama majiyar NAIJ.com cewar dama can ministan mai Ibe Kachikwu baya kaunar Baru ya gaje shi ne:

“Idan aka duba laifukan Baru, babu zargin cin hanci da rashawa, matsalarsa kawai Baru na da hanyar ganin shugaban kasa kai tsaye.

“Kwata kwata Kachikwu bai so Baru ya gaje shi ba, kuma yayi duk iya bakin kokari ya ga ya hana shi zama shugaban NNPC, don kafin yanzu, Baru ne babban Daraktan hako mai da sarrafa shi, amma sai Kachikwu ya rage masa mukami zuwa mai bada shawara akan iskar gas” Inji majiyar, wanda ke da ruwa da tsaki a harkar mai.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Check out the unbelievable state of the National Stadium in Surulere, Lagos, NAIJ.com TV

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel