Wani jigo a jam’iyyar APC, Mustapha ya tona asirin asalin makiyan Buhari

Wani jigo a jam’iyyar APC, Mustapha ya tona asirin asalin makiyan Buhari

- Bode Mustapha ya tona asalin makiyan shugaban kasa Muhammadu Buhari

- Mustapha ya ce masu kira da shugaban kasa ya kara tsaya takara makiyan sa ne

- Tsohon dan majalisar ya shawarci Buhari da ya bi sahun takawaran sa Nelson Mandela

Tsohon dan majallissar dokoki kuma jigo a jam’iyyar APC daga jihar Ogun, Bode Mustapha ya bayyana asalin makiyan shugaban kasa Muhammadu Buhari a yayin da ake tunkarar zaben 2019.

A jawabin da yayi yace, “wadanda suke son Buhari ya kara tsaya takara ba sa son shi, sune asalin makiyan shi."

A zantawar da yayi da yan jaridar Sun Newspaper: Bode ya shawarci Buhari da yabi sahun takwaran sa Nelson Mandela wajen kin kara tsayawa takara bayan ya kammala wa’adin sa na farko a kan mulki.

Wani jigo a jam’iyyar APC, Mustapha ya tona asarin asalin makiyan Buhari

Wani jigo a jam’iyyar APC, Mustapha ya tona asarin asalin makiyan Buhari

“Duk dan Najeriyan da yake bibiyan yadda abubwa su ka gudana a kasar nan a cikin shekara daya da ta gabata, kuma yana kira da Buhari ya kara tsaya wa takara bai da adalci, yana fadin hakane da wata muguyar manufa.

KU KARANTA : Dalilin da yasa Buhari ba zai yi amfani da sakamakon taron gamayyar kasa da Jonathan yasa ayi a 2014 ba

“Duk wanda yake son Najeriya, ba zai shawarci Buhari yakara tsayawa takara ba, musamman idan yayi la’akari da lafiya da shekarun sa.

“Tabbas Buhari yayi kokari wajen yaki da cin hanci da rashawa a kasar nan wanda shine babban kalubale da kasar ta ke fukanta.

“Kuma wannan yana daga cikin nasarar da ya samu a gwamnatin sa, kada ya sauarari masu kiran shi da ya kara tsayawa takara saboda makiyan sa ne.”

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel