Jirgin kasa ya murkushe wasu dalibai yan Indiya uku yayinda suke daukar hoto

Jirgin kasa ya murkushe wasu dalibai yan Indiya uku yayinda suke daukar hoto

- Jirgin kasa ya hallaka wasu daliban makarantar kwaleji guda uku a ranar Talata

- Hatsarin ya afku ne a lokacin da daliban suke daukar hotunan kawunansu

- Kasar Indiya tafi ko wace kasa samun irin wannan mutuwa a duniya

Jirgin kasa ya hallaka wasu daliban makarantar kwaleji guda uku a ranar Talata yayinda suke daukar hounan kawunansu a kasar Indiya, kasar da tafi ko wacce samun irin wannan mutuwa a halin daukar hoto a duniya.

Matasan uku na daukar hotunan kawunansu ne a kwangirin jirgi lokacin da jirgin ya murkushe su a garin Bidadi a kudancin jihar Karnataka, cewar yan sanda.

Jirgin kasa ya murkushe wasu dalibai yan Indiya uku yayinda suke daukar hoto

Jirgin kasa ya murkushe wasu dalibai yan Indiya uku yayinda suke daukar hoto

“Mun gano gawawwakinsu a jikin kwangirin jirgin sannan kuma an gudanar da bincike,” R S Bylanjaiah, wani jami’in dan sandan kwangiri ya fada ma AFP.

KU KARANTA KUMA: Bayan kwanaki 35, mutumin da ya soki Gwamna Masari a Facebook na nan a tsare

Ya ce su ukun sun ajiye ababen hawansu a gefen kwangirin kafin su yi tattaki zuwa tsakiyar kwangirin don daukar hotuna.

Bincike ya nuna cewa duk duniya kasar Indiya tafi samun irin wannan matsala na mutuwa ta hanyar daukar hoto.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel