Majalisar ɗinkin Duniya ta ƙaddamar da shirin samar da abinci na dala miliyan 9 a Kaduna

Majalisar ɗinkin Duniya ta ƙaddamar da shirin samar da abinci na dala miliyan 9 a Kaduna

Majalisar dinkin Duniya ta kaddamar da shirin tallafi ga manoma a ranar Talata 3 ga watan Oktoba a jihar Kaduna don tallafa ma manoman tare da inganta rayuwarsu.

Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito shirin tallafin ya lashe kudi kimanin dala miliyan 9, kamar yadda jami’i mai kula da shirin, Edward Kallon ya bayyana, inda yace taken shirin shine ‘Abincin nahiyar Afirka”, kuma an yi shi ne domin inganta sinadaran abinci a yankin.

KU KARANTA: Mu leƙa Kannywood: Ciwon dake damun jarumin Fim ɗin Hausa Warangis yayi kamari

Bugu da kari, Kallon yace shirin zai samar da isashshen abinci ga jama’an jihar, tare da samar da ayyuka da matasa, sa’annan zai samar ma manoma kudaden shiga tare da rage asarar da suke yi a kaka noma.

Majalisar ɗinkin Duniya ta ƙaddamar da shirin samar da abinci na dala miliyan 9 a Kaduna

El-Rufai

Jami’in ya kara da cewa za’a aiwatar da shirin tare da hadin gwiwa da kamfanoni kamar su gidauniyar MDD mai kula da cigaban muradun karni, cibiyar abinci ta Duniya, kamfanin Sahara, kungiyar kwadago ta duniya, kamfanin Roca Brothers da gwamnatin jihar Kaduna.

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito a karkashin shirin za’a horar da manoma 4000 sabbin hanyoyin noman zamani, inda ko a yanzu ma sun fara da manoma 50.

Haka zalika ita ma gwamnatin jihar ta bakin babban sakataren ma’aikatar noma, Abdulkadir Kassim ya yaba ma MDD data zabi jihar Kaduna don aiwatar da shirin, inda yace wannan nada nasaba da manufar gwamnatin jihar na inganta rayuwar al’ummarta.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Price of petrol crashes in Nigeria, NAIJ.com TV

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel