Hijira: Marasa Lafiya 4 tare mutane 134 sun dawo Najeriya daga kasar Libya

Hijira: Marasa Lafiya 4 tare mutane 134 sun dawo Najeriya daga kasar Libya

A ranar Talatar da ta gabata, akalla mutane 138 suka dawo gida Najeriya daga kasar Libya tare da taimakon kungiyar kaura ta duniya wato International Organisation for Migration (IMO).

Naij.com ta samu rahoton cewa, ma'aikatan cibiyar kawo dauki na gaggawa (National Emergency Management Agency, NEMA) ne suka tarbi wannan ayarin jama'ar sakamakon zaman rashin sanin inda za su sanya kansu a kasar ta Libya da suke yi.

Shugaban cibiyar NEMA reshen Kudu maso Yamma Mista Suleiman Yakubu, ya bayyana cewa jirgin masu kaurar ya sauka ne da misalin karfe 8:05 a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake jihar Legas, inda kuma yace akwai masu fama da matsananciyar rashin lafiya guda hudu a cikin masu kaurar kuma su na bukatar kulawa cikin gaggawa.

Hijira: Marasa Lafiya 4 tare mutane 134 sun dawo Najeriya daga kasar Libya

Hijira: Marasa Lafiya 4 tare mutane 134 sun dawo Najeriya daga kasar Libya

Yakubu wanda ya wakilci Darakta Janar na NEMA Mista Mustapha Maihaja ya bayyana cewa, mutane 138 ne suka dawo gida Najeriya, wadanda suka hadar da mata 65, budurwai 2, mata na goye 2, mazaje 64, samari 2 da kuma maza na goye guda uku.

KARANTA KUMA: Cibiyoyin Jakadancin Najeriya a kasashen ketare su na ganin takansu - Akpabio

A kalamansa, "wadannan mutane 138 da suka yi kaura zuwa kasar ta Libya sun bukaci dawo gida Najeriya ta hanyar neman taimakon kungiyar IOM"

Ya kuma gargadi wadannan mutane akan su sake nazari kuma su yi wa kansu karatun ta nutsu, domin kuwa akwai tanadai da gwamnatin kasar nan take yi wajen inganta zamantakewa da rayuwar al'umma.

Idan ba a manta ba, a watan Satumba da ya gabata, Naij.com ta kawo muku rahoton mata 2 masu juna biyu da kuma mutane 119 da kungiyar ta IOM ta tallafawa wajen dawo dasu kasar Najeriya.

Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59

Shugaba Buhari zaije ziyarar aiki kasar Nijar a gobe litinin don bikin cikar kasar shekaru 59
NAIJ.com
Mailfire view pixel