Majalisar dattijai zata binciki korar sojoji 38

Majalisar dattijai zata binciki korar sojoji 38

- A ranar 16 ga watan yuni da ya gabata ne hukumar soji ta bayyana tursasa wasu jami'anta 38 yin ritayar dole

- Korar jami'an soji 38 daga aiki ta bar baya da kura bayan da daya daga cikin korarrun sojojin ya rubuta takardar korafi ga majalisar dattijai

- Wani binciken manema labarai ya nuna cewar an kori jami'an sojin ba bisa ka'ida ba

Korar jami'an soji 38 daga aiki ya bar baya da kura bayan da daya daga cikin korarrun sojojin, Abdulfatai Mohammed, ya rubuta takardar korafi ga majalisar dattijai ta hannun sanatan APC daga jihar Delta, Ovie Omo-Agege, ranar 19 ga watan yuli.

Majalisar dattijai zata binciki korar sojoji 38

Majalisar dattijai zata binciki korar sojoji 38

Korafin korarrun sojin yana gaban kwamitin majalisar na sauraron korafin jama'a karkashin jagorancin sanata Samuel Anyanwu domin bibcike. kuma aka sanya yau laraba domin sauraren korafin da zai samu halartar jami'an hukamar soji ta kasa da kuma sojojin da suka yi korafin an kore su na bisa ka'ida ba.

DUBA WANNAN: Badakalar Kudi: Kotu ta yankewa wani farfesa hukuncin zaman kurkuku na shekara 40

A ranar 16 ga watan yuni da ya gabata ne hukumar soji ta bayyana tursasa wasu jami'anta 38 yin ritayar dole bisa laifukan nuna rashin da'a da suka aikata lokacin zaben shekarar 2015 da kuma rawar da suka taka a badakalar dala biliyan 2.1 kudin ta kudin makamai.

Wani binciken manema labarai ya nuna cewar an kori jami'an sojin ba bisa ka'ida ba musamman idan aka yi la'akari da yanayin aikin soja, wanda yake da bukatar biyayya ga na sama. Korarrun sojojin sun rubuta korafe-korafe amma basu sami amsa ba har sai yanzu da majalisar dattawa zata binciki maganar.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Canji: Hotunan ƙarin sabbin taragon jirgin kasa na Abuja-Kaduna sun iso Najeriya

Canji: Hotunan ƙarin sabbin taragon jirgin kasa na Abuja-Kaduna sun iso Najeriya

Canji: Hotunan ƙarin sabbin taragon jirgin kasa na Abuja-Kaduna sun iso Najeriya
NAIJ.com
Mailfire view pixel