Yan sanda sun kama diribobin taksi na Uber 2 da zargi yiwa fasinja sata

Yan sanda sun kama diribobin taksi na Uber 2 da zargi yiwa fasinja sata

- Yan sanda sun kama dirobobin taksin Uber da suka kware wajen yiwa fasinjoji mata sata

- Direbobin suna tilasta fasinjojin su zuwa banki da bindiga dan su ciro musu kudi a ATM

- Kwamishinan yansadar jihar Legas ya ba yansadar jihar umarnin kara kaimi

Jami’an yansandar jihar Legas sun kama wasu direbobin taksin Uber biyu da suka kware wajen yi wa fasinjoji mata sata da bindiga.

Jam’ian yansanda na Special Anti Roberry Squad (SARS) sun kama direbobin ne, Fosta Rufus, da Franklin Jogbodo a unguwar Lekki dake Victoria Island jihar Legas.

Kwamishinan yansadar jihar Legas, Imohimi Edgal, yace masu laifin suna tilasta fasinjojin da suka dauka zuwa banki da bindiga dan su ciro musu kudi a ATM.

Yan sanda sun kama diribobin taksi na Uber 2 da zargi yiwa fasinja sata

Yan sanda sun kama diribobin taksi na Uber 2 da zargi yiwa fasinja sata

Direbobin sun amsa laifin da ake zargin su da shi, kuma sun ce da sa hanun su a wasu fashi da aka yi a baya.

KU KARANTA : Dalilin da yasa Buhari ba zai yi amfani da sakamakon taron gamayyar kasa da Jonathan yasa ayi a 2014 ba

“Akwai matar da suka amsa Naira N86,000 a hanun ta da suka yi amfani da ATM din Bankin Access,” inji shi.

Suna amfani da mota, kirar KIA Rio mai lamba BDG 376 EP wurin yin fashi, an samu abubuwa da yawa a cikin motar su wanda ya hada da, wayar Samsung Galaxy 7 edge da kuma iPhone 6 plus wanda suka sace daga hanun wasu fasinjojin su ma su suna Nancy Nzuebo da Eze Chinonso.

Kwamishinan ya ba rundunar yansadar jihar umarni tsayawa a kan manyana hanyoyin jihar dan samar da tsaro.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel