Hukumar EFCC ta sake waiwayar INEC

Hukumar EFCC ta sake waiwayar INEC

- Akwai yiwuwan Hukumar EFCC zata yi kamu a Hukumar INEC a yayin da EFCC din ke binciken Jihohi 20

- Wannan baya ga binkcike da tuni ya ke gudana ne kan jami'an INEC guda 205 da ake zargin karban kudi daga hannun Diezani.

- Shugaban INEC Farfesa Mahmood Yakubu ya ce mutane na da daman yin ma wakilan su kiranyen dawowa gida

A cewar shugaban Hukumar zabe ta kasa (INEC) Farfesa Mahmood Yakubu, Hukumar yaki da cin hanci da rashawa tuni ta fara gudanar da bincike kan jami'an Hukumar ta INEC a Jihohi 20 bisa zargin ha'inci kan al'amurran zabe.

Hukumar EFCC ta sake waiwayar INEC

Hukumar EFCC ta sake waiwayar INEC

Wannan bincike baya ga binciken da EFCC ke gudanarwa ne kan jami'an INEC guda 205 wadanda ake zargi da amfana da naira biliyan 23 da tsohuwar ministar man fetur wato Diezani ta rarraba. Yakubu ya ce za su cigaba da ba EFCC hadin kai koda kuwa ta kama INEC ta canza duk jami'anta ne gaba dayan su.

Shugaban ya ce cikin mutane 2,786,405 suka yi rijistan katin zabe tsaknain watan Afirilu da Satumba na wannan shekara mutum 108,752 kawai suka je suka karbi katin na su. A wandanda suka yi rejistan, Jihar Rivers ke da mafi yawan mutane 151,398, Legas ke da mutum 144,076 sai Ondo da nafi karancin mutum 29,766.

DUB WANNAN: Tabbas doka zatayi aiki kan Evans, Inji Sifeto Janar Idris

A matakin yanki, Kudu maso Kudu ke da mafiya yawan mutane da ya kai 667,103, sai kuma Kudu maso Yamma da mutane 532,172, sannan sai Arewa maso Yamma da mutane 477,056, sai Arewa maso Tsakiya da mutane 374,923, sannan sai Kudu maso Gabas da mutane 352,942. Arewa maso Gabas ce ta karshe da mutane 350,938.

Yakubu ya ce akwai katin zaben mutun guda miliyan 8 da ba'a zo an karba ba a inda fiye da miliyan 1 na 'yan Jihar Legas ne. Ya ce za su ta yin bakin kokarin su duk da matsaloli da suke fuskanta. kuma ya ce mutane na da ikon yin ma wakilan su kiranyen dadawo gida idan wakilcin na su bai gamsar da su ba.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, a tuntube mu a:

labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
INEC ta kori jami'anta 2 akan zargin yi wa gwamnan jihar Kogi rajista so biyu

INEC ta kori jami'anta 2 akan zargin yi wa gwamnan jihar Kogi rajista so biyu

INEC ta kori wasu jami'anta 2 akan yi wa gwamna Bello rajista so biyu
NAIJ.com
Mailfire view pixel