Bayan kwanaki 35, mutumin da ya soki Gwamna Masari a Facebook na nan a tsare

Bayan kwanaki 35, mutumin da ya soki Gwamna Masari a Facebook na nan a tsare

- An kama Ibrahim Bature, matashi mai shekaru 31 dake zaune a Unguwar Dabino, garin Dutsinma dake jihar Katsina kan zargin sukar Gwamna Aminu Masari

- An gurfanar da Bature a gaban kotu sannan an cigaba da tsare shi bayan yan sanda sun kama shi

- An cigaba da tsare shi har bayan kwanaki 35 inda lauyan say ace ana nan ana kokarin ganin an fito da shi

Kwanaki talatin da biyar bayan an kama shi kan zargin sukar Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina a shafin Facebook, matashin mai shekaru 31 Ibrahim Bature na unguwar Dabino, garin Dutsinma, na nan a tsare har yanzu.

Daily Trust ta ruwaito cewa yan sanda sun kama Bature a ranar 28 ga watan Agusta kan ikirarin cewa ya soki gwamnan.

An gurfanar da shi a gaban kotu bisa zargin kokarin haddasa rashin da’a ga gwamnatin Katsina da kuma bata suna.

Rahoton yace Mani Mamman, wani inspekta na yan sanda da aka jona da sashin kwararru na jihar ne ya kama Bature ya kuma kai shi hukumar kafin a tsare shi.

KU KARANTA KUMA: Shugaban hafsan soji ya kaddamar da gagarumin aiki a Maiduguri (hotuna)

Daga baya aka tsare shi a kurkuku.

A cewar bayanan farko na rundunar yan sanda, a watan Yulin 2017 Bature ya wallafa rahoto karya cewa Gwamna Masari na kokarin hallaka makomar jihar ta hanyar karban bashi kimanin naira biliyan 77.7 sanann kuma cewaa gwamnatin na kokarin karban wani bashin na USD 110 don gina asibitoci a kananan hukumomi 34 na jihar.

Lauyan mai laifin, Barista MS Mahuta, ya tabbatar da cewa ana kokarin ganin an sake shi Kan beli.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu
NAIJ.com
Mailfire view pixel