Gwamna El-Rufai da Shugaba Buhari za su yi tazarce - Jam’iyyar APC

Gwamna El-Rufai da Shugaba Buhari za su yi tazarce - Jam’iyyar APC

- Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana irin kokarin Gwamna El-Rufai

- Jam’iyyar APC a Jihar tace Gwamnan zai yi tazarce a zabe mai zuwa

- Gwamna El-Rufai ya bayyana cewa bai ba Shugaba Buhari kunya ba

Mai ba Gwamnan Jihar Kaduna shawara game da harkokin siyasa Uba Sani ya bayyana irin kokari da kuma tafiyar Gwamna Nasir El-Rufai a Jihar Kaduna.

Gwamna El-Rufai da Shugaba Buhari za su yi tazarce - Jam’iyyar APC

Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai

A cewar sa Jam’iyyar APC a Jihar tayi wa Gwamnan da kuma Shugaba Buhari mubaya’a a zaben 2019 saboda irin kokarin da su kayi na kawo gyara a mulki. Kawo yanzu dai Gwamnan ya kawo kamfanunka da za su habaka harkar noma a Jihar wanda har Shugaban kasar ya zo da kan sa.

KU KARANTA: Rashin lafiya ta kwantar da wani Minista

A cewar sa dai Gwamnan Jihar na Kaduna El-Rufai bai ba Shugaban kasa Muhammadu Buhari kunya ba inda har ya neme sa ya sake tsayawa takara a 2019. Mai ba Gwamnan shawara yace akwai lokacin da El-Rufai yace idan Shugaba Buhari ba zai fito takara shi ma ya hakura.

A jiya mun samu labari cewa Kotu ta takawa Gwamnatin Jihar Kaduna burki na korar masu Unguwar da ya tsige daga gidajen su.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel