Harkar noma: Farashin kayan abinci sun sauko a Najeriya Inji Garba Shehu

Harkar noma: Farashin kayan abinci sun sauko a Najeriya Inji Garba Shehu

- Garba Shehu ya bayyana irin aikin da Gwamnatin Buhari ta ke yi

- A cewar mai magana da bakin Shugaban kasar abinci ya yawaita

- Haka nan kuma yace ana dacewa wajen yaki da cin hanci da rashawa

Mai magana da bakin Shugaban kasa watau Garba Shehu yayi tsokaci game da jawabin Shugaba Buhari na Ranar samun 'yancin kai inda yace an fara kai ga ci.

Harkar noma: Farashin kayan abinci sun sauko a Najeriya Inji Garba Shehu

Garba Shehu ya bayyana yadda kayan abinci su ka sauko

Garba Shehu ya bayyana cewa a Gwamnatin Shugaba Buhari yadda abinci ya fara araha saboda habaka harkar noma a cikin gida inda yace babu babban ‘yanci kamar kasa ta noma abin da za ta ci. Garba Shehu yace za a zo lokacin da babu wanda zai yi fama da yunwa a kasar.

KU KARANTA: Mafi yawan ayyukan da mu ke yi gadon Jonathan ne

A wajen maganar yaki da sata Shehu ya kawo misalign abin da ya faru kwanaki a Kotu sa’ilin da Alkali Chuka Obiazor ya nemi wanda ya mallaki katafaren gidan tsohuwar Minista Diezani Allison Madueke amma babu wanda ya iya amsawa wanda wanda yace wannan ya isa nasara.

Kun ji cewa Mai ba Gwamnan Jihar Kaduna shawara game da harkokin siyasa Uba Sani yace Jam’iyyar APC a Jihar tayi wa Gwamnan da kuma Shugaba Muhammadu Buhari mubaya’a a zaben 2019 saboda irin kokarin da su kayi na kawo gyara a mulki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa
NAIJ.com
Mailfire view pixel