Fayose yana kamfen din 2019 ba bisa ka'ida ba - Hukumar INEC

Fayose yana kamfen din 2019 ba bisa ka'ida ba - Hukumar INEC

- Hukumar zabe ta kasa wato INEC ta ce Kamfen din da Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose ke yi bijirewa dokar Hukumar ne

- Shugaban Hukumar wato Farfesa Mahmood Yakubu ya gargadi 'yan siyasa da ajiye kamfen din har sai lokaci ya yi

- A dokar Hukumar ana iya fara yin kamfen ne kwanaki 90 kafin ranar yin zabe

A ranar Alhamis din da ta gabata ne Gwamnan Jihar Ekiti wato Ayodele Fayose ya bayyana kudirin sa na fitowa takaran shugabancin kasan nan a zaben 2019 mai zuwa amma Hukumar INEC tace ba'a kan ka'ida yakeyi ba.

Har wayau wasu 'yan siyasan ma tuni sun fara kamfen na zaben da ke zuwa alhali yin hakan bijirewa dokar Hukumar Zabe ta Kasa ne wato INEC wadda tace ana iya fara kamfen din ne kwanaki 90 gabanin zaben.

Fayose yana kamfen din 2019 ba bisa ka'ida ba - Hukumar INEC

Fayose yana kamfen din 2019 ba bisa ka'ida ba - Hukumar INEC

Shi kuwa Farfesa Mahmood Yakubu wanda shi ne shugaban Hukumar, ya gargadi 'yan siyasa da yin kamfen din zaben 2019 mai zuwa har sai lokaci ya yi.

DUBA WANNAN: Dalilin da yasa jawabin shugaban kasa ya mun dadi - Ben Ayade

A tsarin dokar Hukumar ana iya fara kamfen ne kwanaki 90 kafin ranar zabe. Don haka shugaban Hukumar ya gargadi jam'iyoyi da 'yan siyasa da su dakata har sai Hukumar ta fitar da jadawalin kamfen din.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, a tuntube mu a:

labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel