Tabbas doka zatayi aiki kan Evans, Inji Sifeto Janar Idris

Tabbas doka zatayi aiki kan Evans, Inji Sifeto Janar Idris

- Sifeta Janar na 'yan sanda Ibrahim Idris ya bayyana kokarin da Hukumar sa ta ke yi don tabbatar da an daure Evans

- Idris ya kuma mika godiyar sa ga Majalisar Dattawa kan dokar hukuncin Kisa da suka fitar ga duk wanda aka kama da laifin yin garkuwa da mutane

- Ya kuma ce yin garkuwan ya ragu a wasu wuraren sakamakon farautar su da 'yan sanda ke yi

Sifeta Janar na 'yan sanda wato Ibrahim Idris ya yi wa 'yan Najeriya alkwarin lallai Hukumar sa zata tabbata an daure mai yin garkuwa da mutane mai suna Chukwudumebi Onwuamaegbu wato Evans.

Har ila yau zata tabbata an hukunta wani takwaran Evans din mai suna Henry Chibueze da aka fi sani da Vampire, wanda shima shahararren mai yin garkuwa da mutane ne.

Zan tabbatar doka tayi aiki kan Evans, Inji Sifeto Janar Idris

Zan tabbatar doka tayi aiki kan Evans, Inji Sifeto Janar Idris

Idris ya dau wannan alwashi ne a wani taro na harkan tsaro da a aka yi a garin Uyo na Jihar Akwa Ibom a ranar Talata 3 ga watan Oktoba. A nan ne kuma ya mika godiyar sa ga Majalisar Dattawa kan dokar hukuncin Kisa da suka fitar ga duk wanda aka kama da laifin yin garkuwa da mutane.

KU KARANTA: Majalisa ta umarci ma'aikatar aiyuka data gaggauta cire kunyar rage gudu daga kan hanyoyin Najeriya

Idris kuma ya yabawa jami'an 'yan sanda kan yadda suke farautan 'yan fashi da makami da masu yin garkuwa da mutane a Kudu maso Kudu da kuma kan babban titi tsakanin Abuja da Kaduna. Ya kuma yabawa Soji da 'yan sanda kan yadda suka shawo kan matsalar IPOB.

Idan mai karatu na biye da mu zai tuna Naij.com ta bada rahoton yadda Evans ya gurfana a gaban wani babban kotu a Legas. Naij.com har ta kawo maku bidiyo inda aka tasa keyarsa zuwa kurkukun Kirikiri.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, a tuntube mu a:

labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel