'Yan Majalisar Jihar Ekiti na shirin maka Ibrahim Magu a Kotu

'Yan Majalisar Jihar Ekiti na shirin maka Ibrahim Magu a Kotu

- 'Yan Majalisa Jihar Ekiti sun aikawa Shugaban EFCC Magu takarda

- 'Yan Majalisar sun bayyana cewa kama Kwamishinonin Jihar ya saba doka

- Sun bayyana cewa idan Magu bai shiga taitayin sa ba za a shiga Kotu

Mun samu labari daga Jaridar The Cable cewa a Jihar Ekiti 'Yan Majalisa sun gargadi Ibrahim Magu na EFCC sa cewa za su burma Kotu.

'Yan Majalisar Jihar Ekiti na shirin maka Ibrahim Magu a Kotu

Shugaban Hukumar EFCC Magu da Gwamna Fayose na Ekiti

'Yan Majalisar dokokin Jihar sun bayyana cewa damke wasu Kwamishinonin Jihar da aka yi ya saba dokar kasa da kuma umarnin Kotu inda su kace tabbas akwai wani dan shiri da bita-da-kulli. Kwanaki Hukumar ta cafke wasu Kwamishinonin Jihar da zargin karkatar da wasu kudi.

KU KARANTA: Ministar Jonathan tana shirin dawowa Najeriya domin wanke kan ta

A wasikar da Kakakin Majalisar dokokin Jihar ya sa hannu an yi barazanar shiga Kotu da Magu na EFCC idan bai janye yunkurin na sa ba cikin gaggawa. Majalisar tana mai cewa EFCC na ja ne da Gwamnati da ma mutanen Jihar Ekiti inda tace ba za ta yarda da wannan danyen aiki ba.

Kun ji cewa Shugaban Hukumae INEC ya gargadi 'Yan siyasa da su guji fara kamfen din takarar zaben 2019 ko kuma doka ta hau kan su. Tuni dai Gwamna Fayose ya kaddamar da shirin sa na takara.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Illar cin hanci: Sojan Najeriya ya bindige wani Mahauci a kan ya hana shi N500 na goro (Hoto)

Illar cin hanci: Sojan Najeriya ya bindige wani Mahauci a kan ya hana shi N500 na goro (Hoto)

Illar cin hanci: Sojan Najeriya ya bindige wani Mahauci a kan ya hana shi N500 na goro (Hoto)
NAIJ.com
Mailfire view pixel