Ko ana ha maza ha mata ba za mu dakatar da shirin yi wa Melaye kiranye ba - INEC

Ko ana ha maza ha mata ba za mu dakatar da shirin yi wa Melaye kiranye ba - INEC

- Hukumar INEC tace babu abin da zai hana ta yi wa Sanata Melaye kiranye

- Shugaban Hukumar yace tsarin dokar kasa ta ba 'Yan kasa wannan dama

- Yanzu haka dai ana ta faman shiga Kotu tsakanin Dino Melaye da Hukumar

Mun samu labari daga Jaridar The Cable cewa Hukumar zabe na kasa INEC tace babu ja da da baya wajen yunkurin yi wa Dino Melaye kiranye.

Ko ana ha maza ha mata ba za mu dakatar da shirin yi wa Melaye kiranye ba - INEC

Hukumar INEC ta tasa Melaye a gaba

Shugaban Hukumar zabe na kasa Farfesa Mahmud Yakubu yace duk da ja-in-jar da ake ta samu sun shiga Kotun daukaka kara wanda za su yi maza su dauki mataki. Farfesa Yakubu yace dokar kasa ta ba Jama'a damar yi wa wadanda ke wakiltar su kiranye a tsarin Damukaradiyya.

KU KARANTA: Kotu ta daure wani na shekaru 40 a gidan maza

Farfesa Yakubu yace Hukumar ba za ta saba dokar kasa ba wajen yunkurin kiranyen amma ba babu abin da zai dakatar da ita daga aikin ta. Haka nan Shugaban na INEC ya gargadi 'Yan siyasa da su guji fara kamfen din takarar zaben 2019 ko kuma doka ta hau kan su.

A jiya ne Shugaban Majalisa Yakubu Dogara ya rantsar da sabuwar ‘Yar Majalisa Honarabul Dorathy Mato wanda ta maye gurbin Honarabul Hermen Hembe da aka sallama.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad

Dandalin Kannywood: Atiku ne kadai ke da mabudin gyaran Najeriya - Fati Muhammad
NAIJ.com
Mailfire view pixel