Mun batar da Naira miliyan 177 wajen bayar da cin hanci - Ogunmodede

Mun batar da Naira miliyan 177 wajen bayar da cin hanci - Ogunmodede

Tsohon Darakta Janar na makarantar bincike da koyon aikin noma (Institute of Agricultural Research and Training) Farfesa Benjamen Ogunmodede, ya bayyana cewa shi da wasu mutane biyu da kotu ta gurfanar sun batar da akalla Naira Miliyan 177 wajen bayar da cin hanci ga masu wanzar da shari'a a kasar nan tare da kuma wasu ma'aikata na ma'aikatar kudi ta gwamnatin tarayya.

Mun batar da Naira miliyan 177 wajen bayar da cin hanci - Ogunmodede

Mun batar da Naira miliyan 177 wajen bayar da cin hanci - Ogunmodede

A ranar Talatar da ta gabata ne, wata babbar kotun gwamnatin tarayya dake zaman ta a garin Ibadan na jihar Oyo, ta yanke wa Ogunmodede da wasu ma'aikata biyu na makarantar ta IAR&T hukuncin dauri a gidan kaso har na tsawon shekaru 40 ba tare da ba su zabin biyan wata tara ba.

Kotun ta yanke mu su wannan hukuncin ne sakamakon laifukan almundahana da wawaso akan kudin wadanda albashin ma'aikatan makarantar ne da kuma wasu aikace-aikace. Sauran ma'aikatan biyu su na aiki ne karkashin sashen kula da harkokin kudi na makarantar.

KARANTA KUMA: Shekaru 57 da samun 'yancin kai: Jerin shugabannin kasa da Najeriya ta yi

Naij.com ta fahimci cewa hukumar EFCC ce ta yi ruwa da tsaki wajen kamen wannan mutane ukun da suka hadar da Zacheus Tejumola, Adenekan Clement da shi kan sa Ogunmodede.

A na su jawabin kuma, sun bayyanawa kotu cewa kaso mai tsoka na kudin sun yi amfani da shi ne wajen bayar da cin hanci ga wasu 'yan majalisar wakilai da kuma wasu ma'aikata na ma'aikatar kudi na gwamnatin tarayya, wadanda da suka yi ruwa da tsaki wajen sakin kudaden zuwa ga makarantar.

Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Hotuna: Shugaba Buhari ya dawo daga kasar Faransa inda ya halarci taro a kan dumaman yanayi

Hotuna: Shugaba Buhari ya dawo daga kasar Faransa inda ya halarci taro a kan dumaman yanayi

Hotuna: Shugaba Buhari ya dawo daga kasar Faransa inda ya halarci taro a kan dumaman yanayi
NAIJ.com
Mailfire view pixel