Zaben 2019: APC tana yunkurin sanya Sheriff jagorantar Yankunan Arewa Maso Gabas

Zaben 2019: APC tana yunkurin sanya Sheriff jagorantar Yankunan Arewa Maso Gabas

Naij.com ta kawo muku rahoton cewa, jam'iyyar APC (All Progressive Congress) tana yunkurin sanya tsohon gwamnan jihar Borno Ali Modu Shereiff, a matsayin mai wakiltar jam'iyyar da zai daidaita Yankunan Arewa maso Gabas sakamakon zaben 2019 da yake gabatowa.

Rahotanni daga mambobin jam'iyyar reshen jihar Borno wadanda suka roki kar a bayyana sunayensu sun bayyanawa manema labarai na Daily Post cewa, su na cikin damuwar kasancewar lissafi da kuma shawarwari da jam'iyyar ta APC take kokarin gudanarwa a jihar ta Borno.

A cewar su, dawowar Sheriff zuwa jam'iyyar APC bai wuci abin mamaki ba, domin babu shakka Sheriff yana daya daga cikin masu daukar nauyin jam'iyya sai dai akwai hanzari ba gudu ba a jihar Borno kasancewaar dawowarsa za ta iya janyo rabuwar kan mambobin jam'iyyar.

Zaben 2019: APC tana yunkurin sanya Sheriff jagorantar Yankunan Arewa Maso Gabas

Zaben 2019: APC tana yunkurin sanya Sheriff jagorantar Yankunan Arewa Maso Gabas

Wani mai ruwa da tsaki na jam'iyyar APC reshen jihar Borno ya shaidawa manema labarai na Daily Post cewa, "Sanin kowa ne Sheriff ba zai yiwa shugabancin gwamnan jihar biyayya ba. Kuma muddin jam'iyyar ta ba shi wakilcin shiyyar Arewa maso Gabas, to tabbasa zai fi so ya sanya gudanarwarsa musamman a jihar Borno, wanda hakan zai janyo matsala a tattare damu".

Daga wasu majiyun makusanta Sheriff, sun bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Bornon ya yi wata ganawar sirrance tsakaninsa da shugaban kasa Muhammadu Buhari akan shirye-shiryen jam'iyyar wajen zaben 2019.

KARANTA KUMA: Cibiyoyin Jakadancin Najeriya a kasashen ketare su na ganin takansu - Akpabio

Akwai rahotanni da suke nuna cewa, Sheriff yayi makamanciyar wannan ganawar da shugaban ma'aikatan Buhari Abba Kyari, akan bayyana ra'ayinsa domin a ba shi wakilcin daidaita yankunan Arewa maso Gabas.

Wanda wata majiyar kuma ta bayyana cewa, wannan yunkuri na jam'iyyar ta APC bai wuci sanya Sheriff a matsayin mai lura da duk wani shiri na tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ba, don daman ana cewa akwai yunkurinsa na ficewa daga jam'iyyar a watan Dasumba mai gabatowa.

Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa

Abin da Shugaba Buhari ya fadawa ‘Yan APC na Kasar Inyamurai a Villa
NAIJ.com
Mailfire view pixel