Mun kammala shirin kai hare hare a jihar Ondo – Inji wani ɗan Boko Haram

Mun kammala shirin kai hare hare a jihar Ondo – Inji wani ɗan Boko Haram

Wani dan Boko Haram da aka kama a ranar Lahadi 1 ga watan Oktoba ya bayyana cewa akwai wasu yan Boko Haram yanzu haka da suka kammala shirin kai hare hare jihar Ondo.

Mutumin yace shi ma yana cikin wadanda zasu kai harin, kafin jami’an Yansanda su cimmasa, inda suka yi ram da shi, inji rahoton jaridar Daily Post.

KU KARANTA: Mutuwar wasu ƙananan yara 2 ýan gida ɗaya ya firgita jama’an Legas

Bashir wand makiyayi ne shi, yace Yan Boko Haram sun shigar dashi kungiyar ne yayin wata fita da yayi zuwa daji watanni 8 da suka wuce, kuma yace tun daga wannan lokaci mutane 2 kawai ya kashe.

Mun kammala shirin kai hare hare a jihar Ondo – Inji wani ɗan Boko Haram

Dan Boko Haram

“Asali na dan jihar Nassarawa ne, kuma mahaifina ne ya kore ni sakamakon yadda nake yawan kadaicewa ni ka dai. Waus daga cikin mu sun kutsa kai zuwa yankin kudu maso yammacin kasar nan, kuma akwai wasu manyan masu kudi ne ke bamu makamai.” Inji shi.

Bashir shine mutum na 165 cikin jerin yan Boko Haram da ake nema ruwa a jallo, kuma an kama sh ne a daidai wajen da aka kama dan Boko Haram na 156 da Sojoji ke nema ruwa a jallo.

Shima kwamishinan Yansandan jihar Ondo ya tabbatar da cewa Bashir dan Boko Haram ne, kuma yana daya daga cikin almajiran wani kwamandan Boko Haram mai suna Daffo, daya daga cikin makusantan Shekau.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

We need to understand the Biafra objective, NAIJ.com TV

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Illar cin hanci: Sojan Najeriya ya bindige wani Mahauci a kan ya hana shi N500 na goro (Hoto)

Illar cin hanci: Sojan Najeriya ya bindige wani Mahauci a kan ya hana shi N500 na goro (Hoto)

Illar cin hanci: Sojan Najeriya ya bindige wani Mahauci a kan ya hana shi N500 na goro (Hoto)
NAIJ.com
Mailfire view pixel